Abuja: Gidajen Mai da ake Sayar da Fetur a Kasa da Farashin NNPCL
- A ranar Laraba aka wayi gari a Najeriya da karin kudin man fetur wanda lamarin ya tayar da kura a tsakanin al'umma
- An samu wasu gidajen mai mallakar yan kasuwa da suke sayar da fetur a kasa da farashin kamfanin NNPCL a Abuja
- Legit ta tattauna da wani matukin mota, Lawan Musa domin jin ko akwai wasu gidajen mai da suke da araha da ya sha mai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kamfanin man Najeriya na NNPCL ya kara kudin man fetur a ranar Laraba inda lita ta haura N1,000.
Sai dai duk da haka an samu wasu gidajen mai da farashinsu ya fi araha a kan gidajen fetur mallakar gwamnatin Najeriya.
Jaridar Premium Times ta zaga wasu gidajen mai a birnin tarayya Abuja da suke sayar da fetur a kasa da farashin NNPCL.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farashin man NNPCL a Najeriya
Biyo bayan karin man fetur, kamfanin NNPCL ya rarraba kudin litar mai a bisa jihohi da yankunan Najeriya.
A birnin tarayya Abuja, kamfanin man fetur na NNPCL yana sayar da duk litar man fetur a kan akalla N1,030.
Inda ake sayar da fetur a kasa da farashin NNPCL
1. Gidan man NIPCO
A gidan man NIPCO da ke kan titin Ahmadu Bello kusa da kwanar Bantex ana sayar da litar fetur a kan N1,025.
Legit Hausa ta samu labari a wasu wuraren farashin lita ta kai N1, 080 ranar Alhamis.
2. Gidan man Mobil
Farashin litar fetur a gidan man Mobil da ke kan titin Ahmadu Bello da hanyar Obafemi Awolowo da ke Mabushi da Utako yana kan N1,025.
3. Gidajen mai a hanyar filin jirgin sama
Kazalika gidajen man fetur na NIPCO da Mobil da ke hanyar filin jirgin sama suna sayar da litar fetur a kan N1,025.
An tatttaro bayanai daga gidajen man Abuja na yan kasuwa ne a ranar Alhamis, 10 ga watan Oktoba.
Legit ta tattauna da Lawan Musa
Wani matukin mota, Lawan Musa ya zantawa Legit cewa zuwa yanzu bai ci karo da gidan mai da yake da araha kasa da farashin NNPCL ba.
Lawal ya bayyana cewa ya sha mai a Kano kuma tun daga can har Gombe bai ga wani gidan mai da suke da arahar ba.
TUC ta bukaci a rage kudin fetur
A wani rahoton, kun ji cewa TUC ta bukaci gwamnatin tarayya da ta mayar da farashin fetur kamar yadda yake a watan Yunin 2023.
A wani taron manema labarai a Abuja, kungiyar TUC ta ce ba wai iya mayar da fetur farashin shekarar 2023 ba, ana so ya yi kasa da haka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng