Bayan Watanni, Majalisa Ta Karbi Bukatar Tinubu, Ta Tantance Sabon Shugaban NSIPA
- Watanni biyu bayan nadin Dakta Badamasi Lawal a matsayin shugaban hukumar NSIPA, an tabbatar da mukaminsa a majalisa
- Majalisar Tarayya da ke birnin Abuja ta tabbatar da Dakta Badamasi a yau Alhamis 10 ga watan Oktoban 2024 yayin zamanta
- Dakta Badamasi shi ne ya maye gurbin tsohuwar shugabar hukumar NSIPA, Halima Shehu da aka dakatar kan zargin cin hanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Majalisar Tarayya ta tabbatar da Dakta Badamasi Lawal a matsayin sabon shugaban hukumar jin kai ta NSIPA.
Majalisar ta tabbatar da Badamasi ne yayin zamanta a yau Alhamis 10 ga watan Oktoban 2024 a birnin Tarayya, Abuja.
NSIPA: Badamasi ya maye gurbin Halima Shehu
Tribune ta ce NSIPA hukuma ce da ke karkashin ma'aikatar jin kai da walwala na Gwamnatin Tarayya da ke ba da tallafi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dakta Badamasi shi ya maye gurbin Halima Shehu da aka dakatar kan zargin cin hanci da rashawa a hukumar.
Shugaba Bola Tinubu ya nada Badamasi ne a watan Agustan 2024 bayan dakatar da matashiya, Halima Shehu.
Majalisa ta amince da nadin Badamasi Lawal
An tabbatar da Badamasi ne bayan rahoton da shugabar kwamitin Majalisar a bangaren jin kai, Idiat Adebule ta gabatar a gabanta.
Adebule ta ce Badamasi ya amsa tambayoyi musamman game da abubuwan da suka shafi tallafi da jin kaia cewar Daily Nigerian.
Sanatan Plateau ta Arewa, Diket Plang ya yaba da nadin Dakta Badamasi a matsayin shugaban hukumar jin kai ta NSIPA.
Betta Edu ta magantu kan badakalar N3bn
Kun ji cewa Ministar harkokin jin kai da yaƙi da fatara, ta mayar da martani kan badaƙalar cin hanci da rashawa ta N3bn a hukumar NSIPA.
Dr Betta Edu ta musanta zargin da ake mata na hannu a badaƙalar cin hancin Naira biliyan 3, ta bayyana hakan a matsayin aikin masu yaɗa jita-jita.
Dakatacciyar Ministar ta ce ba ta taɓa neman biliyoyin ba daga hukumar NSIPA tun bayan da ta zama minista har zuwa lokacin dakatar da ita.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng