Karya Farashin Abinci: Gwamna Zai Budewa Talaka Shaguna a Kananan Hukumomi

Karya Farashin Abinci: Gwamna Zai Budewa Talaka Shaguna a Kananan Hukumomi

  • Gwamnatin Katsina ta amince da kawo shirin sayar da abinci a farashi mai sauki a dukkan kananan hukumomin jihar
  • Dikko Umamar Radda ya tabbatar da cewa za a kafa shangunan ne domin sayar da abinci da ake amfani da shi a yau da kullum
  • Gwamnatin Katsina ta ce hakan zai kawo saukin rayuwa ga talakawa da kuma inganta rayuwar al'ummar jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda ya amince da kafa 'Rumbun sauki' a dukkan ƙananan hukumomin jihar.

Rumbun sauki tsari ne da zai ba da damar bude shaguna domin sayar da abinci a farashi mai rahusa ga talakawa.

Kara karanta wannan

'Ka biya mu daga tushe', Sarakuna a Arewa sun roki Tinubu kan biyansu hakkokinsu

Gwamna Radda
Za a kafa rumbun sauki a Katsina. Hoto: Ibrahim Kaula Muhammad
Asali: Facebook

Hadimin gwamna Dikko Umaru Radda, Ibrahim Kaulaha Muhammad ne ya wallafa sakon a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a karya farashin abinci a jihar Katsina

Gwamna Dikko Umaru Radda ya amince da fara sayar da abinci a farashi mai rahusa domin saukakawa talakawa.

Dikko Radda ya ce hakan na cikin kudurinsa na samar da sauki ga al'ummar jihar da suke fama da matsalar tattalin arziki.

Za a kafa rumbunan sauki 38 a Katsina

Gwamna Radda ya ce za a kafa kantin sauki 38 a dukkan kananan hukumomin jihar domin al'umma su samu hanyar sayen abinci mai rahusa.

Dikko Radda ya kara da cewa karamar hukumar Katsina za ta samu rumbunan sauki 3, Daura da Funtua za su samu biyu-biyu.

Za a fadada shirin karya farashin abinci

Gwamnan ya kara da cewa a nan gaba zai fadada shirin karya farashin abinci a dukkan mazabun jihar Katsina.

Kara karanta wannan

EFCC ta shiga matsala da gwamnoni 16 suka maka ta a kotu, an samu bayanai

Dikko Radda ya ce akwai mazabu 361 a jihar kuma sannu a hankali al'ummar kowace mazaba za ta amfana da shirin.

Gwamna Dikko Radda ya gana da Buhari

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda ya kai ziyarar ban girma ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa a Daura.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana dalilin kai ziyarar ga shugaba Muhammadu Buhari kwanaki bayan dawowarsa daga kasar waje.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng