Gyara Fadar Nasarawa: Kotu Ta Kawo Cikas ga Aminu Ado Bayero, Ta Ba Shi Umarni
- Wata babbar kotun Kano ta yi hukunci kan buƙatar gwamnatin jihar ta hana Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, gyara fadar Nasarawa
- Kotun ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Dije Abdu-Aboki ta sake hana shi gyara fadar Nasarawa da yake zaune a cikinta bayan an sauke shi
- Gwamnatin jiha da Majalisar Masarautar Kano ne suka shigar da ƙara a gaban kotun bayan Sarkin na 15 ya fara yunƙurin yi wa fadar gyara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Babbar kotun jihar Kano ta sake hana mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado-Bayero gyaran fadar Nassarawa.
Kotun ta hana gyara Fadar Nasarawa ne a hukuncin da ta yanke ranar Alhamis, 10 ga watan Oktoban 2024.
An shigar da Aminu Ado Bayero ƙara
Masu shigar da ƙarar sun haɗa da gwamnatin jihar Kano, babban lauyan gwamnatin Kano da kuma majalisar masarautar Kano, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu shigar da ƙarar ta hannun lauyansu Rilwanu Umar SAN, sun shigar da ƙarar ne a ranar 12 ga Satumba inda suka buƙaci kotu ta hana Aminu Ado-Bayero, gyara ƙaramar fadar Nasarawa da ke kan titin State Road a Kano.
Wane hukunci kotun ta yanke?
A hukuncin da ta yanke, alƙalin kotun kuma babbar mai shari’a ta jihar Kano, mai shari’a Dije Abdu-Aboki, ta bayyana cewa kotun ta amince da buƙatar masu shigar da ƙara, rahoton The Guardian ya tabbatar.
"Yana da mahimmanci a lura cewa wanda ake ƙara bai ƙalubalanci buƙatar masu shigar da ƙara ba."
- Dije Abdu-Aboki
Tun da farko dai lauyan masu shigar da ƙara ya shaida wa kotun cewa sabuwar dokar masarautun jihar Kano ta 2024 ta tsige Aminu Ado Bayero daga sarauta.
Masu shigar da ƙarar sun buƙaci kotun da ta bayyana fadar a matsayin kadarar gwamnatin jihar Kano da Majalisar Masarautar ba mallakin wanda ake ƙara ba.
Kotu ta hana Aminu Ado yin gyara
A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun jihar Kano ta hana Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, gyara fadar Nasarawa tun farko.
Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Dije Abdu Aboki, ta bayar da umarnin wucin gadin da ya hana Sarkin yin gyara a fadar Nasarawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng