Ministan Tsaro Ya Fadi Abin da Zai Faru ga Masu ba Yan Ta'adda Bayanai

Ministan Tsaro Ya Fadi Abin da Zai Faru ga Masu ba Yan Ta'adda Bayanai

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a dauki mummunan mataki kan mutanen da aka kama da taimaka wa yan ta'adda da bayani
  • Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana mataki da za a rika dauka kan wadanda ba su tuba daga hada kai da miyagu ba
  • Bello Matawalle ya bayyana matakin da za a dauka lokacin da ya sauka a kauyen Gundumi zuwa wasu kananan hukumomin Sokoto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto - Karamin Ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle, ya bayyana cewa dakarun tsaron kasar nan ba za su saurarawa yan ta’adda da masu taimaka masu ba.

Kara karanta wannan

Boko haram: Sanata Ndume ya fadi gaskiya kan kai masa hari

Gargadin na sa na zuwa ne a lokacin da gwamnatin jihar Zamfara ke zarginsa da ba yan bindiga kariya.

Sokoto
Gwamnatin tarayya ta gargadi masu ba 'yan ta'adda bayanai Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Aminiya ta tattaro cewa karamin Ministan ya yi jan kunnen ne a kauyen Gundumi a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa kananan hukumomin Isa da Sabon Birni a jihar Sakkwato a yau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene zai faru da abokan yan ta’adda?

Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi gargadi ga wadanda su ke taimakawa yan ta’adda wajen kai farmaki kan jama’a.

Dr. Bello Matawalle yayi barazanar cewa duk masu mika wa yan ta’adda bayanai za su gamu da ajalinsu.

“Za mu kawar da yan ta’adda:” Matawalle

Karamin Ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle ya yi alkawarin dawowar zaman lafiya kauyen Gundumi a jihar Sakkwato.

“Ina tabbatar muku za ta dawo, za mu kawo wani sansanin soji a nan.

Kara karanta wannan

Yaki zai canza: An dauko salon hana yan bindiga yawo a jihohin Arewa

“Amma ku ji tsoron Allah, wadanda suke ta kira da sanar da ’yan fashi game da zirga-zirgar jami’an tsaro da ma ’yan uwansu su daina daga yanzu."
- Bello Matawalle.

"Za a fatattaki yan ta'adda:" Bello Matawalle

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa ana samun nasarori wajen yaki da yan ta'adda da ta'addancin da ya addabi Arewacin kasar nan.

Karamin Ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle ya kara da bayyana cewa an fito da sababbin dabarun da za su kara dakile yan ta'addan da ke kokarin kai hare-hare yankin Arewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.