Bayan Sayen Fetur da Sauki, Yan Kasuwa Sun Zargi NNPCL da Tsuga Masu Farashi

Bayan Sayen Fetur da Sauki, Yan Kasuwa Sun Zargi NNPCL da Tsuga Masu Farashi

  • Kwana guda da samun karin farashin fetur a kasar nan, dillalan mai sun bayyana cewa su ma kamfanin NNPCL bai bar su ba
  • Shugaban IPMAN na kasa, Abubakar Garima ne ya fadi haka, inda ya ce NNPCL ya kara kudin litar fetur din da ya ke sayar masu
  • Garima ya kara da cewa kamfanin NNPCL ya sanya farashi daban-daban, wanda ya danganta daga inda za a yo dakon fetur din

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos Shugaban kungiyar dillalan man fetur (IPMAN) na kasa, Abubakar Garima ya zargi kamfanin mai na NNPCL da yi masu shigo-shigo ba zurfi kan farashin fetur.

Kara karanta wannan

Karin farashin fetur: NLC ta dauki zafi kan lamarin, ta ja kunnen Tinubu da NNPCL

Alhaji Abubakar Garima ya bayyana cewa NNPCL ya fara sayar masu da kowace litar fetur da tsada daga wuraren dakon fetur din kamfanin a jihar Legas.

NNPCL
IPMAN ta zargi NNPCL da kara mata farashin fetur Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

Shugaban IPMAN ya bayyana haka ne ta cikin shirin Channels Television yayin da ake tattaunawa kan sabon farashin man fetur a kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“NNPCL ya kara farashin fetur” - IPMAN

Jaridar Punch ta ce masu kasuwancin man fetur karkashin kungiyar IPMAN sun bayyana cewa yanzu haka kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya kara masu farashin litar fetur.

Shugaban IPMAN na kasa, Abubakar Garima ya ce kamfanin na sayar masu da kowace lita a kan N1,010 duk da ya na sayo shi a kan N800 – N900 daga matatar Dangote.

IPMAN ta fadi farashin fetur a NNPCL

Kungiyar IPMAN ta ce kamfanin NNPCL ya sanya masa mabambamtan farashi a kan kowace lita daga wurin dakon mansa daban daban.

Kara karanta wannan

Sabon farashin mai: Jerin jihohin da fetur ya fi araha da inda ya fi tsada

IPMAN ta ce ana sayar mata da kowace lita daga wurin dakon mai na Kalaba a kan N1,045, N1,050 a Fatakwal sai N1,040 a Warri.

NNPCL: NLC ta dauki zafi kan farashin fetur

A baya mun ruwaito cewa kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta yi tir da karin farashin fetur da kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya yi a ranar Laraba a dukkanin gidajen mansa.

A ranar Laraba 9 Oktoba, 2024 ne aka tashi da ganin karin farashin litar fetur a gidajen mai mallakin NNPCL daga kusan N897 zuwa sama da N1,000 a fadin kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.