Farashin Fetur: Ministar Tinubu Ta yi Albishir Mai Daɗi ga Yan Najeriya

Farashin Fetur: Ministar Tinubu Ta yi Albishir Mai Daɗi ga Yan Najeriya

  • Ministar harakokin mata, Uju Kennedy Ohanenye ta yi albishir ga yan Najeriya kan halin kuncin rayuwa da ake fama da shi
  • Uju Kennedy Ohanenye ta ce a yanzu haka ana ƙoƙarin shawo kan dukkan matsalolin tattali da yan Najeriya ke fama da su
  • Legit ta tattauna da wani matashi, Abdullahi Adamu Musa domin jin yadda ya ji da albishir Uju Kennedy da yi wa yan Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Anambra - Ministar harkokin mata ta ba yan Najeriya hakuri tare da musu albishir da cewa wahala na dab da karewa.

Uju Kennedy Ohanenye ta ce Bola Tinubu na gyara kurakuren da aka yi a gwamnatocin baya ne kuma nan gaba kadan za a samu canji.

Kara karanta wannan

Yaki zai canza: An dauko salon hana yan bindiga yawo a jihohin Arewa

Ministar mata
Minista ta yi albishir ga yan Najeriya. Hoto: Uju Kennedy Ohanenye
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Uju Kennedy Ohanenye ta yi bayani ne yayin raba tallafin abinci a jihar Anambra.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Minista ta yi albishir ga yan Najeriya

Ministar harakokin mata, Uju Kennedy ta yi albishir da cewa cikin watanni kadan masu zuwa za a fita daga matsalolin tattalin arziki da ake fama da su.

A karkashin haka Uju Kennedy ta bukaci yan Najeriya su kara hakuri da shugaban kasa Bola Tinubu kan kokarin da yake.

Bola Tinubu na gyara inji ministar mata

Ministar matar ta bayyana cewa gwamnatocin baya sun lalata kasar kafin Bola Tinubu ya hau mulki.

Ta ce a yanzu haka Tinubu yana ƙoƙarin sanya farin ciki ga yan Najeriya wajen ganin ya fitar da su daga matsalar tattali.

Minista ta raba tallafin abinci

Punch ta ruwaito cewa a ranar Laraba ministar mata, Uju Kennedy Ohanenye ta raba buhunan shinkafa ga al'ummar jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi dalilin kawo manufofin tattalin da suka jawo wahalar rayuwa

Har ila yau, ministar ta raba tukunyar gas da buhunan taki ga manoma a matsayin tallafi daga gwamnatin tarayya.

Legit ta tattauna da Abdullahi Adamu

Wani matashi a jihar Bauchi, Abdullahi Adamu ya zantawa Legit cewa bai gamsu da alkawarin da ministar mata ta yi ba.

Abdullahi ya bayyana cewa za su gaskata albishir din ne kawai idan suka gani a kasa domin an dade ana fada musu irin haka.

Sarakuna sun kai kuka ga Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa wasu sarakunan gargajiya a Najeriya sun nuna damuwa kan yadda ake samun matsala game da kudin da ake ware musu.

Wasu sarakunan daga jihar Nassarawa sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta rika ba su kasonsu na 5% daga tushe domin yin adalci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng