‘Ya Mutu har Lahira,’ Sojoji Sun Yi Rubdugu ga Dan Sanda, Sun Lakaɗa Masa Duka

‘Ya Mutu har Lahira,’ Sojoji Sun Yi Rubdugu ga Dan Sanda, Sun Lakaɗa Masa Duka

  • Wani dan sanda ya gamu da mugun tsautsayi yayin da ya tare wata mota dauke da soja da bai sanye da kayan aiki a Legas
  • An samu sabani tsakanin sojan da dan sandan wanda har sojan ya kira abokan aikinsa suka lakaɗawa dan sandan duka
  • Rundunar sojin Najeriya ta yi bayanai yayin da manema labarai suka tuntubeta kan zargin kisan da ake cewa sojojin sun yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Ana zargin wasu sojojin Najeriya da kashe wani dan sanda ta hanyar yi masa dukan tsiya.

An ruwaito cewa sojojin sun sun yi wa ɗan sandan jina jina kafin daga bisani a kai shi wani asibiti.

Kara karanta wannan

Boko haram: Sanata Ndume ya fadi gaskiya kan kai masa hari

Legas
Sojoji sun kashe dan sanda a Legas. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Punch ta wallafa cewa lamarin ya faru ne a yankin Ojo Iyana a kan hanyar Iba a jihar Legas da ke Kudancin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene ya haɗa dan sanda da soja fada?

Rahotanni sun nuna cewa wani soja da baya sake da kayan aiki yazo wucewa wajen tashar bas ta Volkswagen a Legas.

Wani dan sanda mai suna Saka Ganiyu ya tare sojan bisa zargin karya dokar tuƙi, abin da ya batawa sojan rai kuma ya kira yan uwansa sojoji ta wayar tarho.

Sojoji sun lakaɗawa dan sanda duka

Biyan kiransu a waya, an yi zargin cewa sojoji sun fito daga barikin Ojo suka fara tafkar dan sandan.

An ruwaito cewa sojojin sun lakaɗawa dan sandan dukan tsiya kuma an kai shi asibitin koyarwa na jami'ar Legas wanda a can ya rasu.

Sojoji sun ce ana bincike kan lamarin

Kara karanta wannan

Tuban Muzuru: Tubabbun Boko Haram sun tsere da makamai, suna barazanar kai hari

Yayin da aka tuntubi kakakin sojoji na barikin runduna ta 81, Olabisi Ayeni ya ce sai sun kammala bincike za su yi bayani.

Manema labarai sun yi kokarin tuntubar kakakin yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin amma bai amsa wayar tarho ba.

Tubabbun Boko Haram sun tsere

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni na nuna wasu daga cikin mayakan kungiyar Boko Haram da suka tuba sun tsere da makaman da aka ba su.

Wasu daga cikin yan ta'addar Boko Haram sun fara barazanar kai munanan hare hare a jihar Borno bayan sun gudu sun koma cikin jeji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng