Karin Farashin Fetur: NLC Ta Dauki Zafi kan Lamarin, Ta Ja Kunnen Tinubu da NNPCL

Karin Farashin Fetur: NLC Ta Dauki Zafi kan Lamarin, Ta Ja Kunnen Tinubu da NNPCL

  • Kungiyar Kwadago ta Najeriya ta NLC ta yi Allah wadai da karin farashin man fetur da NNPCL ta yi a fadin Najeriya
  • Kungiyar ta caccaki kamfanin NNPCL, ta ce bai kamata ya ke yanke farashi ba a matsayinsa na kamfani mai zaman kansa
  • Wannan na zuwa ne bayan kamfanin NNPCL ya kara farashin mai daga N897 zuwa fiye da N1,000 a wasu wurare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar Kwadago ta NLC ta yi magana kan karin kudin man fetur da kamfanin NNPCL yi.

Kungiyar ta yi Allah wadai da matakin kara farashin daga N897 zuwa N1,030 a wasu wurare.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Majalisa ta yi albishir ga yan kasa kan saukar farashin fetur

Kungiyar NLC ta yi Allah wadai da karin farashin man fetur
Kungiyar NLC ta caccaki Bola Tinubu kan karin farashin man fetur. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Nigeria Labour Congress, NLC.
Asali: Facebook

NLC ta shawarci Tinubu ya rage kudin man fetur

Shugaban kungiyar, Joe Ajaero shi ya tabbatar da haka a yau Laraba 9 ga watan Oktoban 2024, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ajaero ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta yi gaggawar janye karin da ta yi inda ya ce babu abin da ta iya sai karin kudi.

Shugaban kungiyar ya ce bai san inda gwamnatin take son kai yan Najeriya ba, ya bukaci ta yi musu bayani, Vanguard ta ruwaito.

Har ila yau, Ajaero ya caccaki kamfanin NNPCL kan karin farashin inda ya ce saba doka ne abin da kamfanin ya yi.

NLC ta caccaki kamfanin man NNPCL

"Bai dace ba a ce kamfani mai zaman kansa NNPCL ke yanke farashin man fetur a lamarin kasuwanci."
"Mu na kalubalantar gwamnati da ta sake zama kan yanayin tsarin tattalin arziki domin fitar da kasa a cikin kangi."

Kara karanta wannan

Ana wayyo da karin farashin fetur da NNPCL ya yi, IPMAN za ta ballo ruwa

"Kan haka, muna kira ga gwamnati da ta yi gaggawar janye wannan karin farashi saboda ba mu san inda ta nufa ba yayin da suke kara talauta al'umma."

- Joe Ajaero

Legit Hausa ta tattauna da wani mai siyar da mai a Gombe kan wannan karin farashin man fetur.

Ismai'l Ahmed ya koka kan halin da ake ciki inda ya ce akwai babbar matsala a Najeriya idan ba a dauki mataki ba.

Isa Abubakar da ke harkar sufuri ya bayyana yadda harkokinsu suka fara tabarbarewa saboda tsadar mai.

Isa ya ce a tun bayan karin kudin mai mutane da dama sun koma tafiyar kafa sai dai idan ya zama dole suke biyan abin hawa.

Matakin NNPCL ya kara farashin mai

Kun ji cewa Kamfanin mai na NNPCL ya tsame kansa daga shiga tsakani a harkar kasuwancin man fetur a matatar Aliko Dangote.

Kamfanin ya dauki matakin domin gudun biyan raran kudi yayin da ya ke shiga tsakanin dillalan mai da kuma matatar Dangote.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.