'Yancin Kananan Hukumomi: Majalisa Ta Cimma Matsaya, Ta Gargadi Gwamnoni

'Yancin Kananan Hukumomi: Majalisa Ta Cimma Matsaya, Ta Gargadi Gwamnoni

  • Majalisar dattawa ta buƙaci gwamnonin Najeriya da su bi umarnin Kotun Ƙoli kan ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi
  • Majalisar dattawan ta cimma wannan matsayar ne yayin zaman da ta yi a ranar Laraba, 9 ga watan Oktoban 2024 a Abuja
  • Shugaban majalisar, wanda ya jagoranci zaman ya ce za su yi gyara domin tabbatar da ƴancin ƙananan hukumomin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta yi magana kan hukuncin Kotun Ƙoli dangane da ƴancin gashin kan ƙananan hukumomi.

Majalisar dattawan ta buƙaci jihohi da su bi umarnin hukuncin Kotun Ƙoli ta hanyar tabbatar da cewa ƙananan hukumomi suna da iko kan kuɗinsu.

Majalisar dattawa ta ja kunnen gwamnoni
Majalisar dattawa ta gargadi gwamnoni kan kananan hukumomi Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Jaridar Tribune ta rahoto cewa majalisar ta cimma wannan matsayar ne a yayin zamanta na ranar Laraba, 9 ga watan Oktoban 2024.

Kara karanta wannan

Bayan Sarkin Gobir, wani Basarake ya sake rasuwa a hannun 'yan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zaman majalisar ya gudana ne a ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio.

Wane gargaɗi majalisar ta yi wa gwamnoni?

Majalisar ta gargaɗi jihohi 36 da ƙananan hukumomi 774 da ka da su yi watsi da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomin, rahoton The Eagle ya tabbatar.

Sanata Godswill Akpabio ya ce majalisar za ta yi gyara ga sassan kundin tsarin mulkin ƙasar nan na shekarar 1999.

Gyaran zai shafi musamman sashe na 162, domin ba da cikakken ƴancin cin gashin kai wajen gudanar da harkokin ƙananan hukumomi a Najeriya.

A kwanakin baya ne dai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci wanda ya ba ƙananan hukumomi a ƙasar ƴancin cin gashin kansu.

Shugaban majalisa ya roƙi ƴan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa ya roki ƴan Najeriya su ƙara haƙuri tare da yi wa ƙasarsu kyakkyawan fata.

Kara karanta wannan

An rasa rayuka bayan 'yan bindiga sun kai wani harin ta'addanci

Godwill Akpabio ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa lokacin farin ciki da walwala na nan tafe ba da jimawa ba, don haka ya roki a ƙara hakuri.

Akpabio ya faɗi haka ne a wani taro da aka shirya a babban cocin ƙasa da ke Abuja a wani ɓangare na bikin cikar Najeriya shekaru 64 da ƴanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng