Shinkafa: An Tsare Janar kan Handame Tallafin Tinubu a Kano, Za a Iya Yi Masa Ritaya

Shinkafa: An Tsare Janar kan Handame Tallafin Tinubu a Kano, Za a Iya Yi Masa Ritaya

  • An cafke tare da tsare wani Janar na soja, M. A Sadik daga jihar Kano kan zargin kwashe kayan tallafi da sauran kayayyaki
  • Rundunar sojoji ta gayyaci Janar din zuwa Abuja domin amsa tambayoyi inda daga bisani aka tsare shi a magarkama
  • Hakan ya biyo bayan korafin sojoji da ke karkashinsa a Kano kan kin raba musu shinkafa da ya yi kamar yadda wasu suka samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Rundunar sojoji da tsare Janar din soja, M. A Sadik kan zargin karkatar da kayan tallafin Shugaba Bola Tinubu.

Ana zargin Sadik da handame shinkafar da aka ware na tallafawa sojoji da siyar da makamai da sauran kayayyakin rundunar.

Kara karanta wannan

Kotu ta tumɓuke dan majalisar wakilai, ta tono maguɗin zaɓe da PDP ta yi

Janar na soja ya shiga matsala kan zargin kwashe kayan tallafin sojoji
Rundunar sojoji ta cafke wani Janar kan zargin handame kayan tallafi da siyar da wasu kayayyaki. Hoto: Nigerian Army.
Asali: Facebook

Ana zargin Janar Sadiq da kwashe tallafi

The Nation ta ruwaito cewa an gayyaci Janar din zuwa birnin Abuja domin amsa tambayoyi inda daga bisani aka tsare shi a birnin Tarayya, Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin Janar Sadiq ya siyar da kayayyaki da suka hada da janareta da wasu motocin rundunar sojoji da sauransu.

Wata majiya daga bangaren rundunar sojoji ta ce ana hasashen za a yi masa ritayar dole ba tare da wani hukunci ba.

Wani mataki za a dauka kan sojan?

"An tsare kwamandan '3 Brigade' da ke Kano, Janar M. A Sadik a Abuja kan zargin kwashe shinkafar tallafi da siyar da makamai da wasu kayayyaki na rundunar."
"A karshe, za a yi masa ritayar dole ba tare da daukar wani mataki ko hukunci kansa ba."

- Cewar majiyar

Rahotanni sun tabbatar da cewa an ware kayan tallafin ne domin tallafawa sojoji duba da halin da ake ciki tun bayan cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Kwace kadarori: An samu koma baya a shari'ar tsohuwar minista da EFCC

Ana hasashen cewa jami'an da ke karkashinsa na zargin Janar din yaki raba kayan tallafin kamar yadda sauran sojoji suka samu shinkafa.

Sojoji sun hallaka yan bindiga a Kaduna

Kun ji cewa Dakarun sojojin Najeriya sun kai wani samame a maɓoyar ƴan bindiga da ke ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Sojojin sun yi nasarar sheƙe ƴan bindiga uku tare da raunata wasu a sansanin da ke ƙauyen Kurmin-Kare a cikin ƙaramar hukumar da ke jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.