Sabon Farashin Mai: Jerin Jihohin da Fetur Ya Fi Araha da inda Ya Fi Tsada

Sabon Farashin Mai: Jerin Jihohin da Fetur Ya Fi Araha da inda Ya Fi Tsada

  • A yau Laraba kamfanin man Nigeria na NNPCL ya kara kudin man fetur duk da al'umma na fama da wahalar tsadar rayuwa
  • Rahotanni sun nuna akwai bambancin farashin man fetur a jihohin Arewacin Najeriya da wadanda suke Kudancin kasar
  • Legit ta tattauna da wani dan acaba domin jin yadda tashin farashin man fetur zai shafi ayyukansu a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kamfanin man Najeriya ya kara kudin man fetur a gidajen man NNPCL a fadin ƙasar nan.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da fuskantar kalubalen rayuwa saboda tashin farashin kayayyaki.

Farashin man fetur
Farashin man fetur a jihohin Najeriya. Hoto: NNPC Limited
Asali: Getty Images

A wannan rahoton, mun tattaro muku yadda farashin man fetur zai kasance a jihohi Arewaci da Kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

"A kashe mu a huta:" Yan Najeriya sun koka da karin farashin litar man fetur

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farashin man fetur a yankunan Najeriya

1. Jihar Legas

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa za a rika sayar da litar man fetur a birnin Legas ne a kan N998.

Legas ita ce jihar da man fetur ya fi sauki a Najeriya saboda kusancinta da matatar Dangote.

2. Jihohin Kudu maso Yamma

Farashin litar man fetur a sauran jihohin Kudu maso Yamma na Yarabawa zai kasance a kan N1,025.

3. Jihohin Kudu maso Gabas

Farashin litar man fetur a jihohi biyar na Kudu maso Gabas da suka hada da irinsu Enugu zai kasance a kan N1,045.

4. Kudu maso Kudu

A jihohin Kudu maso Kudancin Najeriya da suka hada da Rivers, NNPCL zai rika sayar da litar man fetur a kan N1,075 kuma yana cikin yanki mafi tsadar man fetur.

5. Jihohin Arewa maso Yamma

Kara karanta wannan

"Ba dai N1,000 ba kuma": Farashin litar man fetur ya sake tashi a Najeriya

A jihohin Arewa maso Yamma da suka hada da Kano, za a rika sayar da litar man fetur a kan N1,070.

6. Jihohin Arewa ta Tsakiya

Rahoton Aminiya ya nuna cewa za a rika sayar da litar man fetur a kan N1,030 a jihohin Arewa ta tsakiya da suka hada da Filato da Nasarawa.

7. Arewa maso Gabas

Farashin Litar man fetur a jihohin Arewa maso Gabas da suka hada da Gombe, Bauchi, Borno, Yobe, Taraba da Adamawa zai kasance a kan N1,075 kuma yana cikin yanki mafi tsada a Najeriya.

Legit ta tattauna da dan acaba

Wani dan acaba, Adamu Garba ya zantawa Legit cewa karin kudin mai zai kara kawo musu cikas sosai.

Adamu Garba ya bayyana cewa ana samun mutane da suke daina hawa babur idan kudi ya karu sai yan acaba su ta yawo ba tare da daukar fasinja ba.

Karin kudin fetur: Yan Najeriya sun koka

Kara karanta wannan

Abubuwa 3 da suka jawo karamar jami'yya ta buga APC da PDP a kasa a Rivers

A wani rahoton, kun ji cewa mazauna kasar nan sun bayyana takaicin yadda gwamnatin Bola Tinubu ta zuba ido ana samun hauhawar farashin fetur.

Jama'a sun tsinci labarin karin farashin litar fetur daga N897 zuwa N1,030 a babban birnin tarayya Abuja, lamarin da ya jawo bacin ran al'umma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng