Kananan Hukumomi: Majalisar Dattawa Ta Shiga Ganawar Sirri kan Matakin Gwamnoni
- Yayin da ake cigaba da dambarwa kan yancin kananan hukumomi, Majalisar Dattawa ta shiga ganawa kan lamarin a Abuja
- Sanata Tony Nwoye daga jihar Anambra shi ya fara korafi kan kokarin da gwamnoni ke yi na dakile kananan hukumomi
- Wannan na zuwa ne bayan yunkurin Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra domin karbe wani kaso na kananan hukumomi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Mambobin Majalisar Dattawa sun shiga ganawar gaggawa kan yancin kananan hukumomi.
An samu rudani da hayaniya a Majalisar bayan korafin Sanata Tony Nwoye daga jihar Anambra kan neman dakile yancin kananan hukumomi.
Ana zargin gwamnoni da dakile kananan hukumomi
Vanguard ta ruwaito cewa sanatocin Majalisar sun yi zaman ne a yau Laraba 9 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Nwoye ya yi korafi kan yadda gwamnonin jihohi ke kokarin dakile yancin kananan hukumomi da hadin bakin mambobin Majalisunsu.
Sanatan ya zargi gwamnonin da neman tilasta 'yan Majalisar jihohinsu kan kirkirar wata doka kan kudin kananan hukumomi, cewar Punch.
Kananan hukumomi: An kalubalanci Sanata kan korafinsa
Yana kammala bayyana korafinsa sai Sanata Adamu Aliero daga jihar Kebbi da Osita Izunaso daga Imo suka bukaci ya dakatar da abin da ya ke yi.
Sanata Aliero ya bukaci 'yan Majalisar su bar magana kan lamarin tun da abu ne da ya shafi kasa baki daya.
A martaninsa, shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya goyi bayan Sanata Aliero kan maganganunsa game da kananan hukumomi.
Akpabio ya ce ya kamata Majalisar ta mayar da hankali wurin gyaran wasu sassa na dokoki da suka shafi kananan hukumomi.
Gwamna na shirin dakile kananan hukumomi
Kun ji cewa Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles C. Soludo ya bullo da dabarar karbe wani kaso daga cikin kudin kananan hukumomi duk wata.
Gwamnan zai yi amfani da majalisar jiha wajen samar da dokar da za ta tabbatar da shugabannin kananan hukumomi sun ba jiha kudinsu.
Dan majalisar dokokin jihar, Henry Mbachu ya yi tir da yunkurin gwamnan, wanda ya ce hakan karan tsaye ne ga cigaban kananan hukumomi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng