"A Kashe Mu a Huta:" Yan Najeriya Sun Koka da Karin Farashin Litar Man Fetur

"A Kashe Mu a Huta:" Yan Najeriya Sun Koka da Karin Farashin Litar Man Fetur

  • Mazauna kasar nan sun bayyana takaicin yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta zuba ido ana samun hauhawar farashin fetur
  • Jama'a sun tsinci labarin karin farashin litar fetur daga N897 zuwa N1,030 a babban birnin Abuja, lamarin da ya jawo bacin rai
  • Wasu daga cikin mazauna Kano sun bayyana cewa dama ana cikin mawuyacin hali, kuma sabon karin zai kara lalata al'amura

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Labarin karin farashin litar fetur da ya bullo yau Laraba ya jefa mazauna kasar nan a cikin fargaba da bacin rai.

A yau ne kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya kara farashin litar fetur daga N897 zuwa N1,030 a gidajen mansa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

"Haka mu ka ji labari:" 'Yan kasuwa sun fadi matsayarsu kan karin kudin litar fetur

NNPCL
Yan Najeriya sun koka da karin farashin litar fetur Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa sabon farashin litar fetur ya tashi daga N885 zuwa N998 a jihar Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farashin fetur: Daliban Kano sun fara kuka

Wasu dalibai a jihar Kano da su ka zanta da Legit sun bayyana cewa lamarin karin farashin fetur a kasar nan zai jefa iliminsu a cikin barazana.

Maryam, daya daga cikin daliban da ke karatu a jami'ar NOUN, ta bayyana cewa duk da ba kullum ta ke zuwa makaranta ba, amma ta na shan wahala sosai.

"Sai na yi ta tsayar da masu adaidata sahu, amma ba mu daidaitawa, kudin mota ya yi yawa," a cewar dalibar.

Magidanta sun fusata da karin farashin fetur

Faisal Abdullahi, wani mazaunin Kano ne, ya ce karin farashin litar fetur zai shafi magidanta a kasar nan.

A matsayinsa na mai kasuwanci, Faisal na ganin za a kara samun tsadar rayuwa da hauhawar farashi bayan matsin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi dalilin kawo manufofin tattalin da suka jawo wahalar rayuwa

'Yan kasa sun fadi ra'ayinsu kan tashin fetur

Wasu daga cikin masu amfani da shafukan sada zumunta a sun bayyana cewa karin farashin fetur zai kara ta'azzara talauci.

@rolandjick267 ya ce;

“Ta yaya za mu rayu? Lamarin nan ya yi yawa.”

@qudus_kalas ya ce:

“ Kawai a jefa bam a kasar nan kowa ya mutu a huta."

An kara farashin fetur a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa an wayi garin Laraba da samun karuwar farashin litar man fetur a gidajen man NNPCL a dukkanin jihohi da Abuja.

An ga karin farshin litar fetur din ne jim kadan bayan kamfanin ya bayyana cewa ya janye daga zama mai shiga tsakanin yan kasuwa da matatar man Dangote.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.