"Kokarin da Muke domin Rage Kudin Aikin Hajjin 2025": Shugaban NAHCON

"Kokarin da Muke domin Rage Kudin Aikin Hajjin 2025": Shugaban NAHCON

  • Hukumar NAHCON ta yi magana kan ƙoƙarin da take yi domin ganin an rage kuɗin zuwa aikin Hajjin shekarar 2025
  • Shugaban hukumar ya bayyana cewa suna aiki tuƙuru domin ganin Alhazai ba su biya N10m da aka yi hasashen za su biya ba
  • Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya ce hukumar ba ta ƙayyade kuɗin da Alhazan za su biya ba amma suna fatan ka da ya kai na bara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya yi magana kan yiwuwar rage kuɗin aikin Hajjin shekarar 2025.

Farfesa Abdullahi Saleh ya bayyana cewa hukumar na aiki tuƙuru domin ganin an rage kudin aikin Hajjin 2025 wanda aka yi hasashen zai kai Naira miliyan 10.

Kara karanta wannan

Jagora a APC ya sake taso Ganduje a gaba, ya yi masa barazana a jam'iyya

NAHCON na son a rage kudin aikin Hajji
Shugaban NAHCON na kokari a rage kudin aikin Hajjin 2025 Hoto: National Hajj Commission of Nigeria
Asali: Facebook

Ana hasashen maniyyata za su biya N10m

Duk da yake hukumar ba ta bayyana kuɗin aikin Hajjin ba, amma ta tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ba za ta ba da tallafi ba domin aikin Hajjin shekarar 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake zantawa da BBC Hausa, shugaban na NAHCON ya ce hukumar na aiki ba dare ba rana domin ganin an samu raguwar kuɗin da Alhazai za su biya domin zuwa aikin Hajjin 2025.

Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya bayyana cewa hukumar ba ta fatan kuɗin aikin Hajjin su kai N10m.

Wane ƙoƙari hukumar NAHCON ke yi?

"Na farko, wannan ba shi ne fatanmu ba, kuma wannan ba shi ne abin da muke so ya faru ba. Kuma har yanzu ba a kai ga cewa haka ne zai faru ba."
"Mu dai ƙoƙarin da muke yi da shawarwarin da muke bayarwa da waɗanda muke samu muna aiki domin ka da a kai ga hakan. Kuma muna ganin haske. Saboda haka In sha Allahu abin ba zai kai ga hakan ba."

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Wike ya bayyana abin da zai kawo zaman lafiya

"Fatan mu shi ne ma a samu ragowa daga abin da aka biya a bara, kuma wannan shi ne abin da muke aiki ba dare ba rana a kansa. Kuma muna kallon idan Allah ya taimake mu za mu yi nasara."

- Farfesa Abdullahi Saleh Usman

Majalisa ta amince da naɗin shugaban NAHCON

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta tantance Farfesa Abdullahi Sale Usman Pakistan a matsayin shugaban NAHCON.

Majalisar dattawa ta amince da naɗin da Shugaba Tinubu ya yi wa shugaban Izala na Kano domin ya jagoranci hukumar alhazai ta ƙasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng