Gwamna na Neman Tilastawa Kananan Hukumomi Tura Wani Kaso Kudinsu ga Jiha

Gwamna na Neman Tilastawa Kananan Hukumomi Tura Wani Kaso Kudinsu ga Jiha

  • Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles C. Soludo ya bullo da dabarar karbe wani kaso daga cikin kudin kananan hukumomi duk wata
  • Gwamnan zai yi amfani da majalisar jiha wajen samar da dokar da za ta tabbatar da shugabannin kananan hukumomi sun ba jiha kudinsu
  • Dan majalisar dokokin jihar, Henry Mbachu ya yi tir da yunkurin gwamnan, wanda ya ce hakan karan tsaye ne ga cigaban kananan hukumomi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Anambra - Duk da kotun kolin kasar nan ta tabbatarwa kananan hukumomi yancin gashin kai, wanda ke nufin za su rika samun kason kudinsu kai tsaye daga gwamnatin tarayya, za a samu matsala.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi dalilin kawo manufofin tattalin da suka jawo wahalar rayuwa

Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo ya bullo da wata dabara da za ta tilastawa dukkanin kananan hukumomin jiharsa raba kason kudinsu daga gwamnatin tarayya da jihar.

Anambra
Gwamna Charles Soludo na son majalisa ta sahale masa karbar kudin kananan hukumomi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa tuni gwamnan ya fara neman hadin kan majalisar dokokin jihar wajen ganin an yi kashe mu raba tsakanin jihar da kananan hukumomi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna na neman kudin kananan hukumomi

Gwamnan Anambra, Charles Soludo ya mika wani kudiri ga majalisar dokokin jihar domin a ba shi damar samun wani kaso na kudin kananan hukumomi da za su rika samu daga tarayya.

Manufar kudurin shi ne tabbatar da cewa dukkanin shugaban karamar hukuma ya mika wani kaso na kudin da yankinsa zai samu zuwa ga asusun gwamnatin jiha.

Dan majalisa ya yi tir da kudurin gwamna

Dan majalisar dokokin jihar Anambra mai wakiltar Akwa ta Kudu a jam'iyyar LP, Henry Mbachu ya yi tir da kudurin da gwamna Charles Soludo ya mika masu kan kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Yan daba sun cinna wuta a ƙananan hukumomin Rivers, sun yi fashe fashe

Hon. Henry Mbachu ya shawarci gwamnan ya janye kudurin domin wannan ya nuna karara cewa gwamnan na shirin kassara yancin kananan hukumomi na amfani da kudinsu.

Gwamna ya rantsar da Ciyamomi

A wani labarin kun ji cewa gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya rantsar da zababbun shugabannin kananan hukumomi da Kansilolin da su ka yi nasara a zaben Asabar din da ta gabata.

Gwamnan ya gargade sababbin shugabannin da su zama masu gudanar da mulki cikin adalci, sannan ya umarce su da su koma hedkwatar kananan hukumomin domin al'umarsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.