Abin da Ya Sa har Yanzu Dangote bai Fara Sayar da Fetur Kai Tsaye ga Ƴan Kasuwa ba

Abin da Ya Sa har Yanzu Dangote bai Fara Sayar da Fetur Kai Tsaye ga Ƴan Kasuwa ba

  • Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya IPMAN ta ce har yanzu ba ta iya sayen man fetur kai tsaye daga matatar man Dangote
  • Duk da kamfanin man Najeriya ya ce ya janye jiki daga shiga tsakanin Dangote da 'yan kasuwa, IPMAN ta ce NNPC ne ke sayar masu fetur
  • Shugaban IPMAN, Abubakar Maigandi ya nuna cewa har yanzu NNPC ne ke iya sayen mai kai tsaye daga Dangote ban da 'yan kasuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya IPMAN, ta bayyana cewa har yanzu ba ta fara jigilar mai daga matatar Dangote ba.

Kara karanta wannan

Dangote: Gwamnati ta fadi matata 1 da ta amince ta rika samar da man jiragen sama

IPMAN ta ce tana ci gaba da tattaunawa da matatar Dangote game da fara ayyukan dakon mai kuma za ta fara jigilar da zarar an cimma matsaya.

IPMAN ta yi magana kan fara jigilar fetur daga matatar man Dangote
IPMAN ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta fara jigilar mai daga matatar Dangote ba. Hoto: Dangote Group, Wirestock
Asali: Getty Images

Daily Trust ta rahoto kungiyar ta karyata rahotannin baya-bayan nan da ke ikirarin ta zargi Dangote da hana 'ya'yanta sayan mai kai tsaye daga matatarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPCL ya sauya alakarsa da Dangote?

Mun rahoto cewa kamfanin NNPCL ya kawo karshen yarjejeniyar zama abokin huldar daya tilo na matatar Dangote, wanda zai ba ‘yan kasuwa damar sayen mai kai tsaye.

A wata tattauna da BBC Hausa, shugaban IPMAN, Abubakar Maigandi ya ce sanin kowa ne NNPC ne daya tilo da ke sayen mai daga Dangote, inda kungiyar ke saye daga NNPC.

Ya jaddada cewa kungiyar na tattaunawa da shugabannin matatar man Dangote tare da nuna kwarin guiwa game da nasarar tattaunawar.

Kara karanta wannan

Farashin mai ka iya sauyawa da NNPCL ya fasa shiga tsakanin Dangote da dillalai

IPMAN ta magantu kan dakon man Dangote

Abubakar Maigandi ya ce:

"Yayin da nake magana da ku, babu wani tabbaci a hukumance cewa hukumar ta NNPC ta daina aikinta na 'yar tsakiya' a wajen sayen mai daga matatar.
“Ko yau sai da NNPC ya bukaci mu aika da motocinmun zuwa matatar domin dauko fetur, kuma mun bi hakan. Kamfanin ne ya tura bukatunmu ga Dangote."

Ya kuma kara da cewa, “A halin yanzu, ba za mu iya sayen mai kai tsaye daga Dangote ba; dole mu bi ta hannun NNPCL."

Gwamnati ta yi wa Dangote gata

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ce matatar Dangote ce kadai za ta rika sayar da man jiragen sama (Jet A1) ga kamfanonin jirage.

Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya sanar da cewa kamfanonin jiragen saman ne suka amince su rika sayen man daga wajen matatar Dangote kadai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.