Bayan Sarkin Gobir, Wani Basarake Ya Sake Rasuwa a Hannun 'Yan Bindiga

Bayan Sarkin Gobir, Wani Basarake Ya Sake Rasuwa a Hannun 'Yan Bindiga

  • Jami'an tsaro sun yi ƙoƙarin ceto Hakimin Kanya da ke ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a jihar Kebbi wanda ƴan bindiga suka sace
  • Hakimin ya rasa ransa a hannun miyagun ƴan bindigan ne bayan sun yi masa wani rauni a kansa wanda ya yi sanadiyyar rasuwarsa
  • Sai dai bayanai sun ce jami'an tsaron sun iya yin nasarar kuɓutar da sauran mutanen guda takwas da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Hakimin Kanya da ke ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a jihar Kebbi, Alhaji Isah Daya, ya rasu a hannun ƴan bindiga.

Ƴan bindigan dai sun yi garkuwa da Hakimin ne tare da wasu mutane takwas na ƙauyensa a daren ranar Lahadi, 6 ga watan Oktoban 2024.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi artabu da 'yan bindiga, an samu asarar rayuka masu yawa

Basarake ya rasu a hannun 'yan bindiga a jihar Kebbi
Basarake ya rasu a hannun 'yan bindigan da suka sace shi a Kebbi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan bindiga sun hallaka Basarake a Kebbi

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Alhaji Isah Daya ya rasu ne sakamakon raunin da ƴan bindigan suka yi masa a kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tawagar jami'an tsaron rundunar haɗin gwiwa da suka haɗa da sojoji, ƴan sanda, jami'an tsaron fararan hula da ƴan banga sun yi ƙoƙarin ceto Hakimin tare da sauran mutanen da suka sace, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Wani jami'in gwamnati, AbdurRahman Usman Zaga, ya tabbatar da cewa rundunar tsaron ta yi artabu da ƴan bindigan, inda ta yi nasarar kuɓutar da sauran mutane takwas da aka yi garkuwa da su.

Ƴan sanda sun yi ƙarin haske

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kebbi, SP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da mutuwar Hakimin.

SP Nafi'u Abubakar, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa, ƴan bindigan sun yi artabu da tawagar jami’an tsaron a dajin Sakaba, inda aka suka ajiye mutanen da suka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

An rasa rayuka bayan 'yan bindiga sun kai wani harin ta'addanci

Ya bayyana cewa bayan fatattakar ƴan bindigan an gano gawar Hakimin yayin da aka ceto sauran mutanen guda takwas.

Ƴan bindiga sun kashe mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun jefa mutanen ƙauyen Nawfia a ƙaramar hukumar Njikoka ta jihar Anambra cikin jimami.

Miyagun ƴan bindigan sun kashe mutane biyar ne a daren ranar Lahadi, 6 ga watan Oktoban 2024 bayan sun buɗe musu wuta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng