An Rasa Rayuka bayan 'Yan Bindiga Sun Kai Wani Harin Ta'addanci

An Rasa Rayuka bayan 'Yan Bindiga Sun Kai Wani Harin Ta'addanci

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Nawfia da ke cikin ƙaramar hukumar Njikoka a jihar Anambra
  • Ƴan bindigan a yayin harin da suka kai sun hallaka mutum biyar waɗanda ba su san hawa ba kuma ba su san sauka ba
  • Shugaban ƙauyen ya yi kira ga ƴan sanda da su gudanar da bincike domin zaƙulo miyagun da suka yi wannan aika-aikar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Anambra - Ƴan bindiga sun jefa mutanen ƙauyen Nawfia a ƙaramar hukumar Njikoka ta jihar Anambra cikin jimami bayan sun hallaka mutane biyar.

Miyagun ƴan bindigan sun kashe mutanen ne a ranar Lahadi, 6 ga watan Oktoban 2024.

Kara karanta wannan

Sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Kaduna, sun ceto mutane 7 da suka sace

'Yan bindiga sun kai hari a Anambra
'Yan bindiga sun kashe mutane biyar a Anambra Hoto: Legit.ng
Asali: Original

A cikin wata sanarwa a ranar Talata, shugaban ƙauyen, Daniel Okoye, ya yi kira ga ƴan sanda da su gudanar da cikakken bincike kan kisan wanda ya ɗaga musu hankula, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da farko dai ƴan sanda sun bayyana cewa kisan ya auku ne sakamakon faɗan ƴan daba da ake yi tsakanin wasu ƙungiyoyi.

Ƴan bindiga sun yi ta'asa a Anambra

Sai dai, Daniel Okoye ya haƙiƙance cewa babu wata hujjar cewa kisan ya auku ne sakamakon faɗan daba da aka yi.

Ya buƙaci ƴan sandan ka da su yi saurin yanke hukunci ba tare ƙwararan hujjoji ba, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

"A ranar Lahadi, 6 ga watan Oktoba mun shiga jimami bayan ƴan bindiga sun buɗe wuta kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba tare da kashe mutane biyar."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace shugaban makaranta da wasu mutum 8 a Kaduna

"Binciken farko ya nuna cewa ƴan bindigan sun zo ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare a ranar Lahadi a motoci ƙirar Lexus RX da Toyota Sienna, sannan suka buɗe wuta kan matasa a unguwar Umukwa-Umuriam kafin su tsere."

- Daniel Okoye

Ƴan bindiga sun sace mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai hari a garin Kachia a daren ranar Asabar, 5 ga watan Oktoba, suka yi garkuwa da mutane.

A cewar mazauna yankin, maharan sun shiga garin ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare inda suka fara harbe-harbe, lamarin da ya firgita mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng