Dangote: Gwamnati Ta Fadi Matata 1 da Ta Amince Ta Rika Samar da Man Jiragen Sama

Dangote: Gwamnati Ta Fadi Matata 1 da Ta Amince Ta Rika Samar da Man Jiragen Sama

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa matatar Dangote za ta rika samar da man Jet A1 ga kamfanonin jiragen sama na kasar nan
  • Ministan sufurin jiragen sama ya nuna matatar Dangote ce kadai aka amince ta rika samar da man bayan amincewar gwamnati
  • Festus Keyamo ya kuma jaddada cewa gwamnati da Dangote sun fara aiwatar da tsarin sayen mai da Naira domin saukaka cinikiyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa matatar Dangote ce kadai za ta rika sayar da man jiragen sama (Jet A1) ga kamfanonin jiragen sama.

Wannan matakin na zuwa ne awanni bayan kamfanin NNPC ya sanar da cewa ya tsame kansa daga shiga tsakanin matatar Dangote da 'yan kasuwa.

Kara karanta wannan

Dangote ya bayyana tallafin da ya samu wajen gwamnati kan gina matatar mai

Festus Keyamo ya yi magana kan yadda matatar Dangote za ta rika samar da man jiragen sama
Gwamnati ta amince matatar Dangote ta rika samar da man jiragen sama a Najeriya ita kadai. Hoto: Dangote Foundation
Asali: Facebook

Gwamnati ta sake yi wa Dangote gata

Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan a wata tattauna da aka yi da shi a tashar Channels TV a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar ministan, kamfanonin jiragen saman ne suka amince da matatar Dangote ta zamo wacce za ta rika samar masu da man jiragen saman bisa sahalewarsa.

Festus Keyamo ya ce:

"Kamfanonin jiragen sama sun yi ganawa, bisa ga sa albarkata, sun amince za su rika sayen man jiragen sama ne daga matatar Dangote kadai."

Alakar Dangote da gwamnati ta yi karfi

The Nation ta rahoto ministan ya kara da cewa:

"Idan kun lura daga jiha ne muka fara tsarin sayen mai da Naira da matatar Dangote. Wannan harkalla ce ta Naira zalla, babu dala a ciki."
Ya kuma yi karin bayani cewa matakin da kamfanonin jiragen suka dauka ya zo kan gaba saboda Dangote da gwamnatin tarayyar su aiwatar da tsarin sayen mai da Naira.

Kara karanta wannan

NAHCON: Ana fargabar kudin aikin Hajji zai koma N10m a Najeriya, an gano dalili

Ya kuma bayyana cewa wannan shirin da aka yi zai taimaka wajen karawa Naira daraja a kan kudaden kasashen ketare.

NNPCL ya dauki mataki kan matatar Dangote

Tun da fari, mun ruwaito cewa NNPC ya sauya alakarsa da matatar Dangote inda ya ce ya tsame jikinsa daga shiga shamaki tsakanin matatar da 'yan Kasuwa.

Kamfanin man na Najeriya ya bayyana cewa daga yanzu duk wata matatar man kasar za ta iya kulla alakar kasuwanci da dillalai ba tare da ta shiga ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.