Gwamna Zamfara Ya Yi Alhinin Kisan Jami'an Tsaro, Ya Ba da Tabbaci
- Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa kan kisan da ƴan bindiga suka yi wa jami'an Askarawan Zamfara
- Miyagun ƴan binɗigan sun hallaka jami'an tsaron ne a wani harin kwanton ɓauna da suka kai musu a ƙaramar hukumar Tsafe
- Dauda wanda ya nuna alhininsa kan kisan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta tallafawa iyalan jami'an tsaron da aka kashe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya yi alhinin rasuwar jami’an tsaron rundunar Askarawan Zamfara da aka kashe a jihar.
Wasu miyagun bindiga ne suka kashe jami'an tsaron a wani harin kwantan ɓauna da suka kai a yankin Tsafe na jihar Zamfara.
Gwamnan jihar Zamfara ya yi alhini
Gwamna Dauda Lawal ya nuna alhininsa ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Idris, ya fitar a ranar Talata a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Dauda ya bayyana kisan da ƴan bindigan suka yiwa jami'an tsaron a matsayin wani mummunan abu.
Ya yabawa jajircewar jami’an tsaron rundunar Askarawan Zamfara da sauran sojoji bisa sadaukarwar da suke yi wajen kare rayukan jama’a.
Gwamna Dauda ya yi ta'aziyyar Askarawa
"Na samu rahoton wani mummunan harin kwantan ɓauna da ƴan bindiga suka kai jiya a ƙaramar hukumar Tsafe, inda suka kashe jajirtattun jami’an tsaro guda tara."
"Ina so na yi amfani da wannan damar na miƙa ta’aziyyata a madadin gwamnati da al’ummar jihar Zamfara ga iyalai da ƴan uwan jami'an tsaron."
"Ba za a taɓa mantawa da sadaukarwar da suka yi ba. Ina fatan waɗanda suka jikkata za su warke da wuri."
"Gwamnatina ta ƙudiri aniyar bayar da duk wani tallafi da ya dace ga iyalan jami'an tsaron da suka rasa rayukansu."
- Gwamna Dauda Lawal
Gwamna Dauda ya biya kuɗin giratuti
A wani labarin kuma, kun ji gwamna Dauda Lawal ya biya N9bn a matsayin kuɗin giratuti da ma'aikatan Zamfara ke bin bashi tun shekarar 2011.
Gwamna Dauda Lawal ya amince da fara biyan bashin kuɗin giratuti ne waɗanda ake bin jihar bashi a farkon watan Fabrairun 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng