Ku Zo Ku Cike Fom: Tinubu Zai Fara Rabawa Matasa Keke Napep Masu Amfani da CNG
- Ma'aikatar cigaban matasa ta bude shafin da matasa musamman masu sha'awar harkar sufuri za su nemi tallafin Keke Napep da za ta raba
- Ma'aikatar ta ce za ta raba Keke Napep 2,000 masu amfani da gas ns CNG ga matasan kasar karkashin shirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu
- Karamin ministan cigaban matasa, Kwamred Ayodele Olawonde ya yi karin bayanin yadda matasa za su cike fom din shiga cikin shirin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta bude shafin da matasan kasar nan za su iya neman Keke Napep mai amfani da gas din CNG wanda za ta raba nan da dan wani lokaci.
Ma'aikatar ci gaban matasa ta sanar da cewa matasan Najeriya musamman wadanda ke harkar sufuri za su cike fom na neman samun Keke Napep din a shafinta na intanet.
Karamin ministan bunkasa matasa, Kwamred Ayodele Olawonde ya bayyana hakan a shafinsa na X bayan kaddamar da shafin neman tallafin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Tinubu za ta raba Keke Napep
A ranar 1 ga watan Oktoba ne gwamnatin tarayya karkashin shirin shugaban kasa na iskar gas din CNG (P-CNG) ta ce za ta raba Keke Napep 2,000 masu amfani da gas.
Karamin ministan ya ce ta shafin da aka bude, matasa za su hadu da masu aiki kai tsaye da shirin P-CNG yayin da suke kokarin mallakar Keke Napep din.
Ya ce an tsara shafin ne domin ba matasan Najeriya masu yawa damar mallakar adaidaita sahun, tare da sauran shirye shiryen da ya shafi ma'aikatar.
Yadda matasa za su nemi Keke Napep
Ministan ya roki matasan kasar da ke da sha'awar harkar sufuri da kuma shirin Shugaba Bola Tinubu na P-CNG da su cike fom din neman Keke Napep din.
Masu sha'awar samun wadannan Keke Napep, za su shiga shafukan hukumar na yanar gizo kamar haka: www.youthcng.ng ko kuma www.pci.gov.ng/tricycle.
Kwamred Ayodele Olawonde ya kuma yi nuni da cewa manufar shirin Tinubu na Renewed Hope shi ne rage yawan matasa marasa ayyukan yi a fadin kasar.
Ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu na da nufin bunkasa matasan kasar ta hanyar ba su horo kan sana'o'i da kuma ba su kayan jari domin dogaro da kai.
Tinubu ya dauki matakai kan CNG
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya dauki sababbin matakai a kan iskar gas a shirin sauke Najeriya daga turbar dogaro da fetur.
Matakin farko da Tinubu ya dauka shi ne ba da umarnin cewa ma’aikatu da hukumomin gwamnati su koma sayo ababen hawa da ke amfani da iskar CNG.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng