Ba a Gama Koyon Taken Najeriya ba, Gwamnatin Tinubu Ta Kakabawa Ma’aikata
- Gwamnatin Tarayya ta dawo da sabon taken ma'aikatan Gwamnatin Tarayya domin kara musu kaimi da kishin kasa
- Shugabar ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Walson-Jack ta tabbatar da haka inda ta ce hakan yana da fa'ida
- Wannan na zuwa ne bayan Gwmanatin Tarayya ta sauya taken Najeriya wanda har yanzu wasu ke cigaba da koyo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugabar ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Walson-Jack ta sake dawo da taken ma'aikatan Najeriya.
Walson-Jack ta ce an dawo da taken ne domin karawa ma'aikatan Gwamnatin Tarayya karsashi da kuma kishin aiki.
An dawo da taken ma'aikata a Najeriya
Punch ta ruwaito cewa Walson-Jack ta bayyana haka ne a yau Talata 8 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Walson-Jack ta ce hakan zai karawa ma'aikatan kaimi musamman wurin tabbatar da nasarar muradun Bola Tinubu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an kirkiri taken ma'aikatan ne tun a shekarar 2018 domin kara musu kaimi, cewar rahoton ThisDay.
Muhimmancin taken ga ma'aikata a Najeriya
"Mun dawo da taken ma'aikata domin kara musu karsashi wanda za su rika yi da sauran yan Najeriya."
"Taken zai karawa ma'aikatan dagewa kan aikinsu da hana su cin hanci da samar da abin ake nema a aikin."
"Ina amfani da wannan dama domin godewa Bola Tinubu game da goyon baya da yake ba mu wurin kawo sauye-sauye."
- Didi Walson-Jack
Walson-Jack ta bukaci hadin kan ma'aikata wurin tabbatar da yin taken domin kara musu kwarin guiwa.
Gwamnatin Tinubu ta tsara biyan albashin N70,000
Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Tarayya ta fitar da jadawalin abin da kowane ma'aikaci zai samu a sabon mafi ƙarancin albashin da aka kawo.
An kasafta tsarin yadda ma'aikatan gwamnati za mu samu albashi har na tsawon shekara bayan karin kudin da aka yi masu.
Hakan na zuwa bayan rahotanni sun tabbatar da fara biyan mafi ƙarancin albashin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng