Tura Ta Kai Bango: Dattawan Arewa Za Su Nemo Hanyar Magance Matsalar Tsaro
- Kungiyar Arewa Consultative Forum ta bayyana rashin jin dadi kan yadda rashin tsaro da rarrabuwar kai ke kamari a Arewacin kasar
- Sakataren yada labaran na kasa, Farfesa Tukur Muhammad ne ya bayyana haka, inda ya ce yanzu haka an kammala shirin kawo gyara
- Daga cikin abubuwan da ACF ta ke shirin yi akwai kafa kwamitoci biyu da za su nemo hanyoyin warware matsalolin da su ka addabi Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Kungiyar ACF ta bayyana cewa sun fara daukar matakan da za su magance karuwar rashin tsaro da rarrabuwar kai tsakanin mazauna Arewacin kasar nan.
Sakataren yada labarai na kungiyar, Farfesa Tukur Muhammad Baba ne ya bayyana shirin da su ke yi saboda yadda lamarin rashin tsaro ke kamari a wannan yankin.
A hira da ya kebanta da Daily Trust, kungiyar ta ce ta gaji da zura ido tsaro na kara tabarbarewa kuma jama’a na kara nuna kiyayya ga junansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ACF ta kafa kwamiti kan matsalar Arewa
Dattawan Arewa sun hada kai wajen wajen kafa kwamitoci guda biyu domin lalubo hanyoyin magance matsalar rashin tsaro da rarrabuwar kai.
Kungiyar ACF ta ce rashin tsaro da ta’addanci a yankin ya lalata kwanciyar hankali da yan Arewacin kasar nan su ka saba da shi.
Su wanene a kwamitocin da ACF ta kafa?
Kungiyar Arewa ta sanya tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Yayale Ahmed ne zai jagoranci daya daga cikin kwamitin da zai nemo hanyoyin wanzar da zaman lafiya da hadin kai a yankin.
Sai kwamiti na biyu da tsohon babban hafsan soji na kasa, Laftanal janar AbdulRahman Dambazau mai ritaya zai jagoranci yadda za a magance matsalar tsaro a yankin.
Arewa: ACF ta koka kan barazanar tsaro
A baya mun wallafa cewa dattawan Arewa sun bayyana fargabar yadda rashin tsaro ke zama babbar barazana, inda su ke ganin lamarin zai iya shafe yankin.
Shugaban kwamitin amintattun kungiyar, Alhaji Bashir Muhammad Dalhatu ne ya bayyana fargabar da su ke ciki, inda ya ce dole ne a tashi da gaske wajen nemo hanyar magance matsalar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng