Basarake Ya Rasa Ransa da Boko Haram Suka Shammaci Motar Sojoji, An Rasa Rayuka

Basarake Ya Rasa Ransa da Boko Haram Suka Shammaci Motar Sojoji, An Rasa Rayuka

  • Sojoji sun rasa rayukansu yayin da mayakan Boko Haram suka shammace su a karamar hukumar Marte a Borno
  • Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai harin ne da daren ranar Litinin 7 ga watan Oktoban 2024, aka rasa rayuka
  • Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai dagaci da wani shugaban yan sa-kai a karamar hukumar Marte

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Borno - Mayakan Boko Haram a jihar Borno sun kai wani mummunan hari kan rundunar sojoji.

Yayin harin, mayakan Boko Haram sun hallaka basarake da kuma mutane biyar da suka hada da sojoji a karamar hukumar Marte.

Yan Boko Haram sun hallaka basarake da sojoji a Borno
Yan Boko Haram sun hallaka sojoji da wani basarake a jihar Borno. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yaushe Boko Haram suka kai hari a Borno?

Kara karanta wannan

Abubuwa 3 da suka jawo karamar jami'yya ta buga APC da PDP a kasa a Rivers

Daily Trust ta ce harin ya faru ne a daren jiya Litinin 7 ga watan Oktoban 2024 inda mutane da dama suka samu raunuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiyar tsaro ta ce daga cikin wadanda aka hallaka akwai wani shugaban yan sa-kai a karamar hukumar Marte.

Har ila yau, an kwashi wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti domin ba su kulawa na musamman.

Yawan mutanen da Boko Haram suka hallaka

"Mutane biyar suka mutu ciki har da dagaci mai suna Mai Babashehu Mai Musinema da sojoji guda biyu."
"Sannan yan Boko Haram sun hallaka wani shugaban yan sa-kai a karamar hukumar Marte da ke jihar da wasu mutane biyu."
"Sun fara gyaran hanya da ta lalace ga masu ababan hawa tsakanin Marte da Dikwa kwanaki biyu da suka wuce, yanzu sun koma domin karasa aikin sai mayakan suka shammace su."

Kara karanta wannan

"Abin da ake tsoro kenan": Sheikh Gumi kan mummunan akida da yan bindiga suka dauko

- Cewar majiyar

Boko Haram sun kashe manoma a Borno

Kun ji cewa yan ta'addan Boko Haram sun yi garkuwa da wasu manoma a jihar Borno bayan sun kai musu farmaki a gona.

Miyagun ƴan ta'addan sun yi wa wasu daga cikin manoman yankan rago bayan sun tafi da su zuwa sansaninsu da ke jihar.

Harin da ƴan Boko Haram suka kai a ƙaramar hukumar Gwoza ya kuma yi sanadiyyar rasa ran wani jami'in tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.