Asirin Kishiya Mai Ganawa Jarirai Azaba Ya Tonu, Yan Sanda Sun Cafke Ta
- Rundunar yan sanda a jihar Adamawa da ke Arewacin Najeriya sun zargi wata kishiya da laifin azabtar da jarirai bisa zalunci
- An ruwaito cewa matar da ake zargi mai suna Fatima Abubakar tana zaune ne a ƙaramar hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa
- Kakakin yan sanda na reshen jihar Adamawa ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya bayyana matakin da za su dauka a kanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Adamawa - Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Adamawa ta kama wata kishiya kan zargin azabtar da jarirai.
An ruwaito cewa makwabtan matar da ake zargin sun yi shaida a kan mummunan halin da take na cin zalin yara ƙanana.
Jaridar Punch ta wallafa cewa rundunar yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta fara bincike.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama kishiya mai azabtar da jarirai
Rundunar yan sanda a Adamawa sun kama wata mata, Fatima Abubakar bisa zargin azabtar da wasu jarirai biyu da ke karkashin kulawarta.
Ana zargin Fatima Abubakar ne da yi wa jariran horo mai muni duk da kasancewar yaran suna matakin rarrafe ne.
Daily Trust ta wallafa cewa bayanan yan sanda sun nuna cewa jariran sun kasance 'ya'yan kishiyar matar ne.
Menene dalilin azabtar da jariran kishiya
An ruwaito cewa Fatima Abubakar ta yi wa yaran horo mai tsanani ne wai saboda sun yi fitsari da kashi a tsakar gidanta.
Mutanen unguwar sun bayyanawa yan sanda cewa Fatima ta saba aikata haka kuma Allah bai taba ba ta haihuwa duk da tana shekaru 37.
Yan sandan Adamawa za su yi bincike
Rundunar yan sanda ta kara da cewa Fatima ta saba azabtar da yara wajen hana su abinci kuma tana gargaɗin jama'a kan mata katsalandan.
Kakakin yan sanda, Sulaiman Ngurore ya ce matar ta amince da laifin kuma za a mika ta gaban kotu bayan bincike.
An kama matashin da ya kashe dan banga
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sandan Ogun ta cafke wani matashi mai suna Faisal Audu da ake zargi da kashe wani dan banga.
Bayan kisan dan bangar mai suna Saheed Awolesi, an ruwaito cewa Faisal Audu ya sace wasu kayayyakinsa ciki har da babur.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng