‘Za Mu Gama da Su,’ Bayan Rokon Turji, Gwamna Ya Tsaurara Matakai kan Yan Bindiga

‘Za Mu Gama da Su,’ Bayan Rokon Turji, Gwamna Ya Tsaurara Matakai kan Yan Bindiga

  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya kai ziyarar ba-zata wajen da ake ba yan sa-kai horo domin dakile miyagu yan bindiga
  • A yayin ziyarar, gwamna Dikko Umaru Radda ya kara amincewa da daukar yan sa-kai 500 domin cigaba da farautar miyagu a jihar
  • Hakan na zuwa ne bayan ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji ya bukaci a dakatar da yan banga da masu sa-kai idan ana so su ajiye makamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta kara daukan mataki domin cigaba da farautar miyagu masu garkuwa da mutane.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana matakin ne yayin wata ziyara da ya kai sansanin da ake yi wa yan sa-kai horo a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan kone kone a Rivers, ya ba yan sanda zazzafan umarni

Gwamna Radda
Za a kara yan sa-kai a Katsina. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Asali: Facebook

Legit ta samu bayanin da gwamna Radda ya yi ne a cikin wani sako da hadiminsa, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a kara daukar yan sa-kai a Katsina

Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana aniyar daukar yan sa-kai 500 domin ba su horo na musamman su cigaba da yaki da yan bindiga.

Za a dauki yan sa-kan ne daga kananan hukumomi goma da suke fama da matsalar yan bindiga a jihar.

Gwamna Radda ya ziyarci sansanin yan sa-kai

Gwamna Dikko Radda ya kai ziyarar gani da ido a kan yadda ake ba yan sa-kai horo a jihar inda ya yi musu kyautar N5m.

Dikko Radda ya jaddada musu cewa zai yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin an magance matsalolin tsaro da suka addabi Katsina.

An tanadi kayan aiki ga yan sa-kai

Kara karanta wannan

"Abin da ake tsoro kenan": Sheikh Gumi kan mummunan akida da yan bindiga suka dauko

Gwamnatin Katsina ta bayyana cewa a halin yanzu an tanadi dukkan kayan aiki da yan sa-kai za su bukata wajen gudanar da aiki.

A yanzu haka, Gwamna Radda ya ce an tanadi motoci, babura, makamai da kudin alawus da za a rika ba su domin tabbatar da an gama da yan bindiga.

An fara rabon shinkafa a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Bola Tinubu ta fara raba tallafin shinkafa ga mazauna Katsina domin ragewa jama'a radadin yunwa.

Gwamna Dikko Radda ne ya jagoranci kaddamar da rabon buhunhunan shinkafar tare da Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng