"Duk Kanwar Ja ce:" Bola Tinubu Ya Gano Yadda Za a Yaki Rashawa a Najeriya

"Duk Kanwar Ja ce:" Bola Tinubu Ya Gano Yadda Za a Yaki Rashawa a Najeriya

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dora alhakin rashin ci gaba a Najeriya kan yawaitar cin hanci da rashawa
  • Shugaban ya fadi haka ne ta bakin mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, inda ya ce cin hanci babbar matsala ce
  • Ya bankado hanyar da za a bi wajen tallafawa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa domin kakkabe lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana yadda cin hanci da rashawa ya kassara Najeriya da hana ta cigaba.

Shugaba Tinubu ya fadi haka ne a taron da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ta shirya da hadin gwiwar cibiyar nazarin shari’a ta kasa ga alkalai a Abuja.

Kara karanta wannan

Kotu ta hana EFCC gudanar da bincike a wasu jihohi 10, Olukoyede ya yi bayani

Bola Tinubu
Shugaba Tinubu ya nemi hadin kai don magance cin hanci Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa shugaban da ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashim Shettima ya yi takaicin halin da rashawa ta jefa Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rashawa: Bola Tinubu ya fadi manufar gwamnati

Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC), ta wallafa cewa shugaba Tinubu ya ce a shirye gwamnatinsa ta ke wajen kawar da rashawa.

Shugaban kasar ya ce cin hanci da rashawa ta ratsa dukkanin sassan Najeriya kuma ta shafi kowane dan kasa, lamarin da ya kara munana al'amura.

Tinubu ya nemi taimakon magance rashawa

Gwamnatin Najeriya ta ce dole sai kowane dan kasa ya yi hobbasa wajen ganin an kakkabe cin hanci da rashawa a tsakanin al'uma.

Shugaba Bola Tinubu ya jaddada cewa yaki da rashawa ba aikin hukumomin yakar cin hanci a kasa ba ne kawai, su ma yan kasa sai sun taimaka wajen yakin.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

Tinubu na shirin dakile rashawa

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana hanyar da za ta bi wajen inganta yaki da cin hanci da rashawa ba tare da a samu matsala ba a fadin kasar nan.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce gwamnatin Bola Tinubu ba za ta rika tsoma baki a cikin yadda hukumomin yaki da rashawa ke gudanar da ayyukansu ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.