Majalisa Ta Dakatar da Shugaban Karamar Hukuma, Ta Fadi Dalilin Raba Shi da Ofis

Majalisa Ta Dakatar da Shugaban Karamar Hukuma, Ta Fadi Dalilin Raba Shi da Ofis

  • Majalisar dokokin jiha ta ɗauki matakin ladabtarwa kan ɗaya daga cikin shugabannin ƙananan hukumomin Legas
  • Ƴan majalisar sun dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Alimosho, Jelili Sulaimon bisa wasu zarge-zarge da suke yi masa
  • Sun cimma matsayar cewa mataimakin shugaban ƙaramar hukumar zai ci gaba da tafiyar da harkokin ta bayan dakatarwar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Majalisar dokokin jihar Legas ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Alimosho, Jelili Sulaimon, daga kan muƙaminsa.

A cewar ƴan majalisar, dakatarwar da aka yi wa shugaban ƙaramar hukumar za ta fara aiki ne nan take ba tare da ɓata wani lokaci ba.

Majalisa ta dakatar da ciyaman a Legas
Majalisar dokokin Legas ta dakatar da shugaban karamar hukuma Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Majalisar dokoki ta dakatar da ciyaman

Kara karanta wannan

Bayan Fubara, wani gwamnan ya rantsar da ciyamomin APC, ya ba su shawarwari

Jaridar Tribune ta rahoto cewa ƴan majalisar dokokin sun dakatar da Jelili Sulaiman ne a yayin zamansu na ranar Litinin, 7 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A zaman da suka yi na ranar Litinin, ƴan majalisar sun yanke shawarar cewa mataimakin shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Akinpelu Johnson, ya karɓi ragamar tafiyar da harkokinta, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Majalisar ta kuma umarci mahukuntan ƙaramar hukumar da suka haɗa da manaja da ma’aji da su amince da ikon mataimakin shugaban tare da ba shi dukkanin goyon baya domin ya gudanar da aikinsa yadda ya kamata.

Meyasa aka dakatar da ciyaman a Legas

Ƴan majalisar dai sun dakatar da Sulaiman Jelili ne daga muƙaminsa bayan sun kaɗa ƙuri'ar amincewa ta bai ɗaya kan ƙudirin neman a dakatar da shi.

Ana dai zarginsa ne da rashin bin dokoki, bijirewa da rashin biyayya ga majalisar.

Kara karanta wannan

Ana cikin tsadar rayuwa Tinubu ya fadi lokacin da 'yan Najeriya za su gode masa

Gwamna ya rantsar da ciyamomin APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya rantsar da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi 23 na jihar da ke yankin Arewa ta Tsakiya.

Gwamna Alia ya rantsar da shugabannin ƙananan hukumomin ne a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoban 2024 a gidan gwamnatin jihar da ke Makurdi.

Alia ya buƙace su da su yi aiki tare da ƴan adawa ta hanyar karɓar shawarwari da gyare-gyare masu ma'ana domin samar da shugabanci nagari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng