Matatar Dangote: NNPCL Ya Dauki Matakin da zai iya Jawo Sauyin Farashin Fetur

Matatar Dangote: NNPCL Ya Dauki Matakin da zai iya Jawo Sauyin Farashin Fetur

  • Kamfanin man Najeriya na NNPCL ya yi karin haske kan yadda alakar kasuwanci za ta cigaba da kasance tsakaninsa da matatar Dangote
  • NNPCL ya ce a yanzu haka ya jefar da ƙwallon mangoro wajen shiga tsakiya tsakanin matatar Dangote da yan kasuwar man fetur
  • Hakan na nuna cewa matatar Dangote za ta rika sayar da man fetur ga yan kasuwa a farashin da suka daidaita a tsakaninsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kamfanin man fetur na NNPCL ya fitar da sabuwar sanarwa kan alakarsa da matatar Dangote.

NNPCL ya ce zai daina shiga tsakanin yan kasuwa da matatar Dangote a kan abin da ya shafi cinikin mai

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara rabawa matasa Keke Napep 2000 marasa amfani da fetur

Dangote
NNPCL ya daina shiga tsakani kan man fetur a matatar Dangote. Hoto: Dangote Industries|NNPC Limited
Asali: UGC

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa NNPCL ya ce duk wata matata a Najeriya za ta iya kulla ciniki da yan kasuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matatar Dangote: Majalisa ta yi kira ga NNPCL

Tun a ranar 26 ga Satumba majalisar wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya kan NNPCL da matatar Dangote.

Majalisar ta bukaci gwamnati ta tilasta kamfanin NNPCL ya cire hannu kan shiga tsakanin yan kasuwa da matatar Dangote.

Dan majalisa daga jihar Bayelsa, Hon. Oboku Oforji ne ya gabatar da kudirin a gaban majalisar wakilai inda ya ce ba adalci a cikin lamarin.

NNPCL ya dauki mataki kan matatar Dangote

Kamfanin NNPCL na gwamnatin tarayya ya ce zai ajiye matsayin mai shiga tsakani a harkar cinikin mai a matatar Dangote.

NNPCL ya ce daga yanzu yan kasuwa za su iya kulla ciniki tsakaninsu da matatar Dangote ba tare da katsalandan ba.

Kara karanta wannan

1 Oktoba: Bayan lissafo matsaloli, gwamna ya fadi abin da ake bukata daga yan Najeriya

Yiwuwar saukar farashin man fetur

Masana na ganin hakan zai iya kawo saukar farashin man fetur a gidajen man Najeriya kasancewar za a samu gasa a tsakanin yan kasuwa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa biyo bayan hukuncin, fetur ya sauko daga N1,300/1,350 zuwa N1,200/1,150 a jihar Abia.

Farashin danyen mai ya tashi a duniya

A wani rahoton, kun ji cewa farashin gangar danyen mai ya tashi a duniya bayan harin ramuwar gayya da Iran ta kai kasar Isra'ila.

An ji shugaban kasar Amurka, Joe Biden yana cewa ana tattauna martanin da Isra'ila ta yi da kuma duba yiwuwar kai hari Iran.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng