Farfesa Pantami Ya Fadi Matsayar Musulunci kan ba Shugabanni Rigar Kariya
- Tsohon Ministan sadarwa na kasa, Farfasa Isa Ali Pantami ya bayyana rashin amfanin rigar kariya ga shugabanni
- Farfesa Pantami ya bayyana haka ne a taron 'Muslim Congress' da ke gudana duk shekara a babban birnin tarayya Abuja
- Malamin ya ce ko a musulunci babu rigar kariya ga shugabanni, kowa zai iya fuskantar shari'a idan ya ba daidai ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Tsohon Ministan sadarwa na kasa, Farfesa Isa Ali Pantami ya shawarci gwamnatin Najeriya da ta sake duba batun bayar da kariya ga shugabanni.
Ya bukaci haka ne domin tabbatar da gaskiya a tsarin tafiyar da mulkin jama'a a kasar nan a lokacin da ake zargin wasu da almundahana.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Farfesa Pantami ya yi kiran ne a taron shekara-shekara na 'Muslim Congress (TMC)'.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi wa taron taken 'Gina ingantacciyar kasa: Hakki ne kan shugabanni da mabiya domin ta ya Najeriya murnar cika shekaru 64 da samun yanci.
"Babu rigar kariya a musulunci:" Farfesa Pantami
BBC Hausa ta wallafa cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya shawarci gwamnatin Najeriya da ta cire rigar kariya da ake ba wa shugabanni a lokacin da su ke mulki.
Ya bayyana cewa babu wani abu mai kama da rigar kariya a addinin musulunci, domin shugabanni da mabiya za su iya fuskantar hukunci idan sun aikata ba daidai ba.
Farfesa Pantami bai ganin amfanin rigar kariya
Tsohon Ministan na sadarwa a gwamnatin Muhammadu Buhari ya bayyana cewa rigar kariya ga shugabanni ba ta da amfanin komai.
“Kuma idan ka bar ofis, sai ka ga bayan shekaru hudu ko takwas an bijirowa mutum da tuhume-tuhume 10, 50, har 120 ga wasu,"
- Sheikh Isa Ali Pantami.
Talauci: Farfesa Pantami ya bayar da mafita
A wani labarin, kun ji cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana yadda alkaluma su ka tabbatar da yan kasar nan sama da miliyan 88.4 na cikin talauci.
Pantami ya koka kan yadda aka gano adadin masu fama da talaucin a Arewacin kasar nan su ke, kuma ya shawarci matasa su rungumi fasahar zamani.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng