Ribas: Mummunar Gobara Ta Babbake Sakatariyar Karamar Hukuma, Bayanai Sun Fito

Ribas: Mummunar Gobara Ta Babbake Sakatariyar Karamar Hukuma, Bayanai Sun Fito

  • Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ba a san ko su wanene ba, sun cinna wuta a sakatariyar karamar hukumar Eleme da ke jihar Ribas
  • An ce zababben ciyaman na Eleme ne tare da kansiloli da magoya bayansa suka tarar da an babbake wasu gine gine na sakatariyar
  • Zuwa yanzu dai babu wata sanarwa daga rundunar 'yan sanda a hukumance amma ana fargabar barkewar rikici a sassan Ribas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ribas - An cinna wuta a wani sashe na sakatariyar karamar hukumar Eleme da ke jihar Ribas awanni bayan rantsar da sababbin ciyamomi.

An ce sabon zababben ciyaman na Eleme, Hon. Brain Gokpa ya isa sakatariyar tare da kansiloli da magoya bayansa amma ya taras da an kona wasu gine-ginen a cikinta.

Kara karanta wannan

Ribas: Gwamna zai rantsar da 'yan jam'iyyar adawa da suka lashe zaben ciyamomi

Gobara ta tashi a sakatariyar karamar hukuma a jihar Ribas
Ana zargin bata gari sun kona sakatariyar karamar hukuma a jihar Ribas. Hoto: @SimFubaraKSC
Asali: Twitter

An sanya wuta a sakatariyar Ribas

Tsohon Jakada, Ambasada Oji Ngofa wanda ya fito daga karamar hukumar Eleme ne ya shaida hakan ga Channels TV a tattaunar da aka yi da shi ta wayar tarho.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin cewa wasu 'yan adawa da zababben shugaban karamar hukumomin da aka rantsar ne suka sanya wutar domin nuna adawarsu a fili.

Ya zuwa yanzu dai ba a kama wani mutum ba, kuma har yanzu rundunar ‘yan sandan ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.

Sai dai rahotonanni sun bayyana cewa akwai fargabar yiwuwar barkewar rikici a wasu kananan hukumomin jihar biyo bayan rantsar da sababbin ciyamomin.

Duba wasu labaran game da jihar Ribas:

Bakuwar jam'iyya ta lashe kujerun ciyamomi 22 a zaben kananan hukumomin Ribas

Fubara zai rantsar da zababbun ciyamomi 23 da aka zaba daga jam'iyyun adawa

Kara karanta wannan

Fargabar barkewar ambaliya: Gwamnati ta aika sakon gaggawa ga mazauna jihar Kwara

Ribas: Fubara ya dakile 'yan sanda daga 'sace' kayayyakin zaben ciyamomi

Zaben ciyamomi: Masu zanga zanga sun mamaye ofishin hukumar zabe ta Ribas

Fubara ya rantsar da ciyamomi a Ribas

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya rantsar da sababbin ciyamomin kananan hukumomi 23.

Sufeto Janar na 'yan sanda, Kayode Egbetokun, ya umarci a janye dukkanin jami'an rundunar daga sakatariyoyin kananan hukumomin jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.