Gobara: Daga Dawowa Kano, Aminu Ado Bayero Ya Ziyarci Kantin Kwari

Gobara: Daga Dawowa Kano, Aminu Ado Bayero Ya Ziyarci Kantin Kwari

  • Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya bayyana takaici kan gobarar da ta tashi a kasuwar Kantin Kwari
  • Jim kadan bayan dawowarsa daga ziyarar aiki da ya kai Abuja, Sarki Ado Bayero ya nufi Kantin Kwarin
  • Daruruwan masoya ne su ka tarbe shi yayin da ya zagaya inda iftila'in gobarar ta afku domin gane wa idanunsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Mai martaba sarkin Kano 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi takaicin iftila'in gobara da ta afkawa wasu shaguna a Kantin Kwari da ke jihar.

Da yammacin Asabar ne wata gobara ta tashi a Gidan Inuwa Mai Mai layin Bayajidda da ke kasuwar sayar da kaya ta Kantin Kwari a Kano.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi illar gobarar kasuwa ga Kano, Abba ya yi wa 'yan kasuwa alkawari

Bayero
Sarki Aminu Ado Bayero ya kai ziyarar jaje Kantin Kwari Hoto: Abubakar Balarabe Kofar Na'isa
Asali: UGC

A bidiyon da wata mai amfani da shafin X, Future Minister ta wallafa, an gano Alhaji Ado Bayero na zagawa ta inda gobarar ta afku domin mika jajensa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aminu Bayero ya yi jajen gobarar Kantin Kwari

Sakataren yada labaran Mai Martaba Sarki na 15 Bayero, Abubakar Balarabe Kofar Na'isa ya tabbatar wa Legit cewa Sarkin ya kai ziyara Kantin Kwari bayan dawowarsa daga ziyarar aiki a Abuja. Ya ce daruruwan masoya ne su ka tarbi Aminu Ado Bayero a Kantin Kwarin saboda jin dadin jajen da ya kai masu da kansa ba sako ba kan gobarar da ta tashi a kasuwar.

Aminu Bayero ya yi addu'a kan gobarar Kantin Kwari

Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi addu'ar Allah ya mayar da asarar da yan kasuwar Kantin Kwari su ka yi. A ziyarar jaje da ya kai kasuwar, Aminu Ado Bayero ya kara da addu'ar Allah Ya kiyaye afkuwar irin wannan iftila'in a nan gaba.

Kara karanta wannan

ACF: Kungiyar dattawa ta fadi yadda rashin tsaro ke neman shafe Arewa

Kano: Gobara ta tashi a Kantin Kwari

A baya mun ruwaito cewa wata gobara ta tashi a kasuwar Kantin Kwari a jihar Kano, inda ta jawo wa yan kasuwa asara, duk da ba a tabbatar da adadin asarar ba.

Shugaban kungiyar yan kasuwar ta Kantin Kwari, Balarabe Tatari ya tabbatar da afkuwar gobarar, inda ya ce sun samu dauki daga hukumomin kashe gobara na Kano da ta tarayya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.