'Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta da Wasu Mutum 8 a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta da Wasu Mutum 8 a Kaduna

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi ta'asa bayan sun kai hari a garin Kachia da ke jihar Kaduna a yankin Arewa maso Yamma
  • Ƴan bindigan sun kai harin ne a cikin dare yayin da suka riƙa harbe-harbe, lamarin da ya firgita mutanen garin
  • Tantiran ƴan bindigan sun yi awon gaba da shugaban makarantar sakandire a garin tare da wasu mutum takwas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun kai hari a garin Kachia a daren ranar Asabar, inda suka yi garkuwa da mutane tara.

A cewar mazauna yankin, maharan sun shiga garin ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare inda suka fara harbe-harbe, lamarin da ya firgita mutane.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace babban basarake da wasu mutane a Kebbi

'Yan bindiga sun kai hari a Kaduna
'Yan bindiga sun sace shugaban makaranta a Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta ce wani mazaunin garin mai suna Hamza Idris, ya shaida mata cewa, mutane sun gudu kafin ƴan bindigan su kai ga inda suka yi niyyar zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane nawa ƴan bindiga suka sace?

Al’ummar garin sun ce wanda ƴan bindigan suka zo ɗauka, Ibrahim Tasi’u Imam, shi ne shugaban makarantar sakandiren gwamnati da ke Kachia kuma sun sace shi ne a gidansa.

Ibrahim Tasi'u Imam malami ne mai wa'azin addinin musulunci ne a babban masallacin Juma'a na birnin Kachia kuma yana aiki a matsayin sakataren ƙungiyar Musulunci ta Fityanul Islam.

A cewar mazauna garin sauran waɗanda lamarin ya ritsa da su sun haɗa da Alhaji Falalu, matarsa, da ƴaƴansa maza biyu, da Alhaji Haladu Hamisu da ƴaƴansa maza biyu.

Wani ƙaramin yaro almajiri da ke kusa da wajen na daga cikin waɗanda ƴan bindigan suka yi awon gaba da su.

Kara karanta wannan

Wasu miyagu sun buɗe wuta a kusa da gidan Ministan Tinubu, sahihan bayanai sun fito

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya ci tura, domin har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba a same shi a waya ba.

Ƴan bindiga sun sace basarake

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi garkuwa da Hakimin Kanya da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a jihar Kebbi.

Miyagun ƴan bindigan sun sace Alhaji Isah Daya ne a ranar Asabar, 5 ga watan Satumban 2024 bayan sun kai farmaki a ƙauyen Kanya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng