'Yan Bindiga Sun Sace Babban Basarake da Wasu Mutane a Kebbi

'Yan Bindiga Sun Sace Babban Basarake da Wasu Mutane a Kebbi

  • Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu da ke jihar Kebbi a yankin Arewacin Najeriya
  • Ƴan bindigan a yayin harin da suka kai a ranar Asabar, 5 ga watan Oktoban 2024 sun yi awon gaba da mutane da dama a ƙauyen Kanya
  • Daga cikin waɗanda ƴan bindigan suka yi garkuwa da su bayan sun kai farmakin har da Hakimin Kanya, Alhaji Isah Daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi garkuwa da Hakimin Kanya da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a jihar Kebbi.

Miyagun ƴan bindigan sun sace Alhaji Isah Daya ne a ranar Asabar, 5 ga watan Satumban 2024.

Kara karanta wannan

An samu asarar rayuka bayan 'yan bindiga sun yiwa jami'an tsaro kwanton bauna

'Yan bindiga sun kai hari a Kebbi
'Yan bindiga sun sace basarake a jihar Kebbi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda ƴan bindiga suka kai harin

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ƴan bindigan sun sace Alhaji Isah Daya ne bayan sun kai hari a ƙauyen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindigan ɗauke da makamai sun kuma kashe mutum ɗaya tare da raunata mutane uku waɗanda yanzu haka suna jinya a asibiti.

Ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da mutane takwas da suka haɗa da basaraken a harin na baya-bayan nan.

Harin na zuwa ne dai kwanaki kaɗan bayan ƴan bindiga sun yi garkuwa da shugaban jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar Suru a jihar.

Ƴan sanda sun yi ƙarin haske kan lamarin

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kebbi, SP Nafiu Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Legit Hausa.

Ya bayyana sunan wanda ƴan bindigan suka hallaka a yayin harin a matsayin Sherrif Alhaji Almu.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun kutsa daji sun sheke babban ɗan bindiga, sun ceto wani Sarki

A cewarsa, rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro ƙarƙashin jagorancin ƴan sanda ta ƙaddamar da farautar ƴan bindigan domin kuɓutar da mutanen da suka sace.

"Eh duk da basaraken mutum tara suka sace sai kuma suka kashe mutum ɗaya. Muna ci gaba da ƙoƙari domin ganin mun kuɓutar da su tare da cafke waɗanda suka yi garkuwa da su."

- ASP Nafiu Abubakar

Ƴan bindiga sun kori masallata

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun yan ta'adda sun kutsa garin Dan-Ali da ke karamar hukumar Dan Musa inda su ka fatattaki masu gudanar da sallar Juma'a.

Ƴan bindigan sun shiga garin Dan Ali su na harbin kan mai uwa da wabi, wanda ya firgita mutanen garin da masallatan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng