N77,000: NYSC Ta Fadi Dalilin Kasa Fara Biyan Sabon Alawus
- Hukumar yi wa ƙasa hidima ta Najeriya (NYSC) ta bayyana dalilin kasa fara biyan sabon alawus ga masu yi wa ƙasa hidima
- Shugaban hukumar NYSC, ya bayyana cewa ba a fara biyan N77,000 ba ne saboda har yanzu gwamnati ba ta saki kuɗaɗen ba
- Birgediya Janar Yusha'u Ahmed ya bayyana cewa yana sa rai nan ba da jimawa za a fara biyan sabon ƙarin na alawus ga masu yi wa ƙasa hidima
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban hukumar yi wa ƙasa hidima ta Najeriya (NYSC), Birgediya Janar Yusha'u Ahmed, ya yi ƙarin haske kan dalilin rashin fara biyan sabon alawus ga masu yiwa ƙasa hidima.
Shugaban na NYSC ya bayyana cewa an samun jinkiri wajen fara biyan sabon alawus ɗin ne saboda har yanzu gwamnati ba ta sakarwa hukumar kuɗin yin ƙarin ba.
A cikin watan Satumba ne dai hukumar NYSC ta fitar da sanarwar yin ƙari a alawus ɗin masu yi wa ƙasa hidima daga Naira 33,000 zuwa 77,000.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa NYSC ba ta biya N77,000 ba?
A yayin wata hira da jaridar BBC Hausa, shugaban na NYSC, ya bayyana cewa duk da cewa an amince da yin ƙarin, har yanzu gwamnati ba ta saki kuɗi ba domin aiwatar da ƙarin na sabon alawus.
"Ba ma su yi wa ƙasa hidima kaɗai ba, har ma'aikatan hukumarmu an yi musu ƙarin kusan wata huɗu zuwa biyar, amma ba a fara biyansu ba, amma muna sa rai nan ba da jimawa ba, za a fara biya, amma har yanzu ba a sakar mana kuɗin ba."
''Bayanin da muka samu bai fayyace mana cewa yaushe za a fara biya ba, amma dai an tabbatar mana cewa an yi musu ƙari daga ranar 29 ga watan Yulin 2024."
- Birgediya Janar Yusha'u Ahmed
Shehu Sani ya buƙaci a yi wa mata ƙarin kuɗi
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya ce kamata ya yi gwamnatin tarayya ta ƙarawa mata ƴan NYSC alawus daga N33,000 zuwa N100,000.
Sanata Shehu Sani ya yabawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu bisa ƙara alawi na matasa masu yi wa ƙasa hidima watau NYSC zuwa N77,000.
Asali: Legit.ng