'Ba Ni Kadai ba ne', Malamin Musulunci Ya Fadi Wadanda Ke Raka Shi Wurin Yan Bindiga

'Ba Ni Kadai ba ne', Malamin Musulunci Ya Fadi Wadanda Ke Raka Shi Wurin Yan Bindiga

  • Babban malamin Musulunci, Sheikh Ahmed Mahmud Gumi ya yi magana kan sulhu da yan bindiga a Arewacin Najeriya
  • Sheikh Gumi ya bayyana wadanda ke masa rakiya zuwa wurin yan bindiga inda ya ce bai taba zuwa shi kaɗai ba
  • Shehin malamin daga bisani ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta nemo tushen matsalar domin samar da hanyar dakile rashin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Sheikh Ahmed Gumi ya yi magana kan kokarinsa a sulhu da yan bindiga.

Sheikh Gumi ya ce bai taba zuwa wurin yan bindiga shi kadai ba inda ya ce ya san me yake yi.

Sheikh Gumi ya magantu kan sulhu da yan bindiga
Sheikh Ahmed Gumi ya shawarci Gwamnatin Tarayya kan shawo kan matsalar yan bindiga. Hoto: Dr. Ahmed Abubakar Mahmud Gumi.
Asali: Facebook

Ta'addanci: Sheikh Gumi ya magantu kan sulhu

Kara karanta wannan

"Abin da ake tsoro kenan": Sheikh Gumi kan mummunan akida da yan bindiga suka dauko

Shehin malamin ya bayyana haka ne yayin hira da jaridar Punch a yau Lahadi 6 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Gumi ya ce mafi yawan lokuta yana samun rakiya ne daga jami'an tsaro da kuma wakilan gwamnati.

Malamin ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta samo tushen matsalar domin kawo karshen lamarin cikin sauki.

Sheikh Gumi ya fadi masu masa rakiya

"Abin da na ke so yan Najeriya su gane shi ne ban taba zuwa wurin yan bindiga ni kadai ba."
"Ina samun rakiyar jami'an gwamnati ne da yan sanda, mutum ba zai je wannan wuri shi kadai ba."
"Sai dai akwai wurin da za su ce kada a zo da su, a wannan lokaci ina zuwa da sarakunan gargajiya ko jami'an gwamanti."

- Sheikh Ahmed Gumi

Sheikh Gumi ya ce babban burinsa shi ne a samu sulhu da zai kawo zaman lafiya, idan sun ba da kofa, sai a zauna da su.

Kara karanta wannan

'Ba a saurare shi ba,' Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu kan jawabin 1 ga watan Oktoba

Sheikh Gumi ya koka da salon yan bindiga

Kun ji cewa fitaccen malamin Musulunci a jihar Kaduna, Sheikh Ahmed Gumi ya nuna damuwa kan ayyukan yan bindiga.

Sheikh Gumi ya ce yanzu yan ta'addan sun sauya salon fadansu inda ya ce abin da ake tsoro kenan tun farkon lamarin.

Malamin ya ce yan bindigan sun dauko salon yaki irin na Boko Haram inda ya ce har yanka mutane suna yi da cin zarafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.