Ambaliya Ta Tafka Barna a wata Jihar Arewa, Gidaje 80 Sun Dulmiye a Cikin Ruwa

Ambaliya Ta Tafka Barna a wata Jihar Arewa, Gidaje 80 Sun Dulmiye a Cikin Ruwa

  • An samu afkuwar ambaliyar ruwa a karamar hukumar Langtang ta Kudu da ke jihar Filato bayan saukar ruwan sama na kwanaki uku a jere
  • An rahoto cewa ambaliyar ruwa ta lalata akalla gidaje 80 musamman a garin Sabon Gida lamarin da ya tilasta mutanen neman mafaka
  • Sakataren kungiyar cigaban al’ummar Sabon Gida, Yintim Nimilam ya roki gwamnatin Filato ta kai masu daukin gaggawa kan ambaliyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Akalla gidaje 80 ne suka lalace a lokacin da ambaliyar ruwa ta afkawa wasu al'ummomi a karamar hukumar Langtang ta Kudu a jihar Filato.

An rahoto cewa ambaliyar ruwan ta afku ne biyo bayan mamakon ruwan sama da aka sha a yankin na tsawon kwanaki uku daga Juma'a zuwa Lahadi.

Kara karanta wannan

Fargabar barkewar ambaliya: Gwamnati ta aika sakon gaggawa ga mazauna jihar Kwara

An samu afkuwar ambaliyar ruwa a wasu yankunan jihar Filato
Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 80 a jihar Filato bayan mamakon ruwan sama. Hoto: Audu Marte
Asali: Getty Images

Filato: Ambaliya ta lalata gidaje 80

Lamarin dai ya jefa al’ummar yankin cikin rudani da firgici inda akasarin wadanda lamarin ya shafa suka nema mafaka inji rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin Angwan Bwarat da ke garin Sabo Gida, Nandul Solomon ya bayyana cewa:

“Kodayake, ambaliyar ba ta jawo asarar rayuka ba, amma saboda tana da girma, ta raba iyalai sama da 80 da muhallansu."

Hakazalika, sakataren kungiyar cigaban al’ummar Sabon Gida, Yintim Yohanna Nimilam, ya koka da yadda ambaliyar ta yi barna mai yawa a yankin.

An roki gwamnati ta kai dauki

Mista Yintim Yohanna Nimilam ya tabbatar da cewa mazauna yankin da dama sun rasa matsugunansu yayin da wasu suka nemi mafaka a gidajen 'yan uwansu da abin bai shafa ba.

Mista Nimilam ya roki gwamnatin jihar Filato da sauran hukumomin da abin ya shafa da su kai daukin gaggawa ga mutanen da lamarin ya shafa.

Kara karanta wannan

Cuta ta ɓarke a jihar Borno bayan ambaliyar ruwan da ta afku, bayanai sun fito

"Muna kira ga gwamnatin jihar Filato da hukumomin da abin ya shafa da su kawo mana dauki."

- A cewar Mista Nimilam.

Ana fargabar ambaliya a Kwara

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kwara ta aika sakon gaggawa ga mazauna yankunan tekuna da su koma garuruwan tudu sakamakon fargabar ambaliyar ruwa.

An tattaro gwamnati ta ba da shawar ne bayan da aka kwashe kwanaki biyar ana zabga ruwan sama a jihar da ya jawo aka samu afkuwar ambaliya a wasu yankuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.