"Abin da Ake Tsoro Kenan": Sheikh Gumi kan Mummunan Akida da Yan Bindiga Suka Dauko
- Fitaccen malamin Musulunci a jihar Kaduna, Sheikh Ahmed Gumi ya nuna damuwa kan ayyukan yan bindiga
- Sheikh Gumi ya ce yanzu yan ta'addan sun sauya salon fadansu inda ya ce abin da ake tsoro kenan tun farko
- Malamin ya ce yan bindigan sun dauko salon yaki irin na Boko Haram inda ya ce har yanka mutane suna yi da cin zarafi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Sheikh Ahmed Gumi ya koka kan yadda yan bindiga suka sauya salo a ayyukansu.
Malamin ya ce a yanzu miyagun sun bar yakin kabilanci inda ya ce sun koma kamar mayakan Boko Haram a Arewa maso Gabas.
Sheikh Gumi ya tsorata da ayyukan ta'addanci
Sheikh Gumi ya fadi haka ne yayin hira da jaridar Punch da aka wallafa a yau Lahadi 6 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehin malamin ya ce tun farko abin da ake gudu kenan ga shi yanzu abin na kokarin fin ƙarfin gwamnati.
Ya ce wannan salo da suka dauko zai yi matukar wahala su ajiye makamansu cikin sauki kamar yadda ake zato.
Sheikh Gumi ya ce miyagun sun sauya salo
"A yanzu sun fara kiran 'Allahu Akbar', wannan shi ne abin da muke tsoro tun farko."
"Yanzu sun fara aikata miyagun ayyuka na kisa da cin zarafin mata da kuma yanka mutane."
"Lokacin da muka je wurinsu ba su kiran 'Allahu Akbar', yanzu sun sake fusata suna ganin yakin daukar fansa suke yi, wannan shi ne abin da muke tsoro daman."
- Dr. Ahmed Abubakar Gumi
Shehu Sani ya yabawa Matawalle kan ta'addanci
Mun baku labarin cewa Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yabawa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle kan yaki da ta'addanci.
Shehu Sani ya kuma bukaci al'umma da su bar sukar Matawalle da Nuhu Ribadu inda ya ce hakan na kawo cikas a yaki da ta'addanci.
Sanatan ya bukaci al'umma da su cigaba da ba da goyon baya domin ganin an kawo karshen rikicin ba sukar su kan lamarin ba.
Asali: Legit.ng