Kano: Gobara Ta Tashi a Kasuwar Kantin Kwari, Ta Tafka Barna
- An samu tashin gobara a babbar kasuwar Kantin Kwari da ke cikin birnin Kano a daren ranar Asabar, 5 ga watan Oktoban
- Gobarar wacce ta tashi da wajen ƙarfe 7:00 na dare ta yi sanadiyyar ƙona wasu daga cikin shagunan da ke cikin kasuwar
- Shugaban ƴan kasuwar wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce an samu nasarar kashe ta kafin ta yaɗu sosai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - An samu tashin gobara a babbar kasuwar Kantin Kwari da ke cikin ƙaramar hukumar Kano Municipal a jihar Kano.
Gobarar wacce ta tashi a daren ranar Asabar ta ƙone shaguna da dama a babbar kasuwar.
Yadda gobarar ta tashi
Jaridar The Punch ta ce gobarar wacce ta fara tashi da misalin ƙarfe 7:00 na dare, ta fara ne a titin Gidan Inuwa Mai Mai Bayajidda, ta kuma shafi gine-gine da dama a tsakiyar kasuwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar, Balarabe Tatari ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Ya bayyana cewa, ɗaukin gaggawar da hukumar kashe gobara ta tarayya, hukumar kashe gobara ta jihar Kano, da wasu kamfanoni masu zaman kansu suka kawo, ya hana gobarar yaɗuwa sosai.
"Ɗaukin gaggawa da hukumar kashe gobara ta jihar Kano da hukumar kashe gobara ta tarayya da kuma wasu ƙarin jami'ai daga wasu kamfanoni masu zaman kansu da kasuwannin Sabon Gari da Dawanau da Singa ya sa aka kashe gobarar."
- Balarabe Tatari
Balarabe Tatari ya kuma ƙara da cewa jami’an hukumar tsaro ta DSS, ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro sun kasance a wajen domin samar da tsaro a kewayen kasuwar.
Me hukumomi suka ce?
Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin.
"Eh gaba ɗaya gobarar ta shafi shaguna 13 ne. Guda biyu sun ƙone yayin da sauran guda 11 gobarar ta ɗan taɓa su ne kawai."
- Saminu Yusuf Abdullahi.
Gobara ta tashi a ofishin ƴan sanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata mummunar gobara ta tashi a hedikwatar rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Sokoto.
Gobarar wacce ba a iya tantance musabbabinta ba, ta tashi ne a safiyar ranar Asabar, 14 ga watan Satumban 2024, ta kone ofisoshi shida a hedikwatar rundunar ‘yan sandan.
Asali: Legit.ng