"Akwai Kiristoci Yan Kasa a Arewa: CAN Ta Koka da Mukaman Hukumar NWDC da Aka Nada
- Kiristoci a yankin Arewa maso Yamma sun nuna damuwa kan yadda aka yi wariya a mukaman hukumar NWDC
- Shugaban kungiyar CAN a yankin, Sunday Oibe ya ce an ware Kiristoci a hukumar raya yankin Arewa maso Yamma
- Oibe ya koka kan haka inda ya ce yankin yana dauke da Kiristoci yan kasa ba wai Musulmai zalla ba ne ke rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kungiyar Kiristoci ta sako Hukumar raya yankin Arewa maso Yamma ta NWDC a gaba kan nadin mukamai.
Kungiyar ta koka kan yadda aka nuna wariya wurin cire sunayen Kiristoci a kwamitin gudanarwa na hukumar NWDC.
NWDC: Kiristoci sun yi korafi a Arewa
Shugaban kungiyar a yankin, Sunday Oibe shi ya tabbatar da haka a jiya Asabar 5 ga watan Oktoban 2024, cewar rahoton TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Oibe ya ce rashin saka sunayen Kiristoci a hukumar ya nuna wariya ƙarara saboda bambancin addini a yankin.
Ya ce akwai Kiristoci yan asalin jihohin Kano da Kaduna da Zamfara da Kebbi da Jigawa da Katsina, cewar rahoton Punch.
Kiristoci sun fadi tasirinsu a Arewacin Najeriya
"Kiristoci a yankin Arewa maso Yamma sun damu kwarai da yadda aka yi nadin muƙaman, nade-naden sun saba da bambancin addini da muke da shi a yankin."
"Akwai Kiristoci yan kasa a jihohin Kano da Kaduna da Jigawa da Katsina da Sokoto da Kebbi da Zamfara."
"Bai kamata a yi tsammanin duka yankin Arewa maso Yamma Musulmai ba ne kaɗai."
- Sunday Oibe
Tinubu ya nada mukamai a hukumar NWDC
Kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa ƴan majalisar gudanarwa a hukumar raya Arewa maso Yamma watau NWDC a ranar Asabar 28 ga watan Satumbar 2024.
Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a wata sanarwa, ya ce ana sa ran waɗanda aka naɗa za su ba da gudummuwa wajen bunƙasa yankin
A watan Yulin 2024 ne Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu a kudirin dokar kafa hukumar NWDC bayan Majalisa ta amince.
Asali: Legit.ng