"Ba na Maganar 2027": Tinubu Ya Magantu kan Zabe, Ya Fadi Abin da Ke Gabansa a Yanzu

"Ba na Maganar 2027": Tinubu Ya Magantu kan Zabe, Ya Fadi Abin da Ke Gabansa a Yanzu

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana matsalarsa kan zaben 2027 da wasu ke ta shirye-shirye domin neman takara
  • Tinubu ya ce shi a yanzu ya mayar da hankalinsa ne wurin kawo sauyi a Najeriya domin inganta rayuwar al'umma
  • Wannan na zuwa ne yayin da wasu yan siyasa daga ɓangarorin Najeriya ke ta shirye-shiryen zaben 2027 tun yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan zaben 2027 da ake ta shirye-shirye.

Tinubu ya ce a yanzu ko kadan bai damu da zaben 2027 ba saboda nemo hanyar kawo sauyi a Najeriya.

Tinubu ya fadi abin da ya dame shi yanzu ba maganar 2027 ya ke yi ba
Bola Tinubu ya ce yanzu inganta Najeriya ne a gabansa ba zaben 2027 ba. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

2027: Tinubu ya bayyana abin da ke damunsa

Kara karanta wannan

Fitattun 'yan siyasar Kudancin Najeriya da za su iya kalubalantar Tinubu a 2027

Shugaban ya fadi haka ne yayin wani taro da jiga-jigan jam'iyyar APC a yau Asabar 5 ga watan Oktoban 2027, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Vanguard ta ruwaito cewa shugaban ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Femi Gbajabiamila ne ya wakilce shi.

Tinubu ya ce a yanzu ya himmatu wurin tabbatar da inganta tattalin arzikin Najeriya domin saukakawa yan kasa.

Shugaban ya bukaci karin hakuri daga yan Najeriya domin samar da ababan more rayuwa da kawo sauyi.

Tinubu ya samu goyon bayan jiga-jigan APC

Wannan na zuwa ne yayin da jiga-jigan jam'iyyar APC a yankin Kudu maso Yamma suka yi taro na musamman inda suka goyi bayan Tinubu kan zaben 2027.

Daga cikinsu akwai gwamnonin jihohin Kudu maso Yammacin Najeriya da tsohon shugaban APC, Cif Bisi Akande.

Taron ya samu halartar manyan-manyan mutane da yan siyasa musamman daga yankin da Tinubu ya fito.

Kara karanta wannan

Bayan bidiyon Bello Turji, Tinubu ya tura gargadi ga yan ta'adda, ya ba su zabi 2

Tinubu ya shirya korar Ministoci a Najeriya

Kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya gama tsara sunayen ministocin da zai ci gaba da aiki da su da waɗanda zai sallama daga aiki.

Wasu rahotanni daga fadar shugaban ƙasa sun nuna tun ranar Alhamis aka yi tsammanin Tinubu zai saki sunayen amma ya canza shawara.

Yanzu haka dai shugaban kasa yana birnin Landan na kasar Burtaniya inda ya tafi hutun shekara na tsawon mako biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.