Kaico: Ana Tsaka da Cin Amarci, Ango Ya Kashe Amaryarsa Ta Hanya Mai Ban Tausayi

Kaico: Ana Tsaka da Cin Amarci, Ango Ya Kashe Amaryarsa Ta Hanya Mai Ban Tausayi

  • Ana zargin wani matashi da bai jima da aure ba, Motunrayo Olaniyi da cakawa amaryarsa wuƙa har lahira a jihar Legas
  • Kakakin ƴan sandan jihar, Benjamin Hundeyin ya ce lamarin ya faru ne ranar Juma'a a yankin Okorodu
  • Ya ce angon ya aikata wannan ɗanyen aiki ne bayan wata taƙaddama ta haɗa shi da amaryar, ya caka mata wuƙa kuma ya banka mata wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Wani matashin ango ɗan kimanin shekara 30, Motunrayo Olaniyi ya daɓawa sabuwar amaryarsa, Olajumoke wuƙa har lahira a jihar Legas.

Lamarin ya faru ne a rukunin gidajen Amazing Grace Estate da ke Elepe a yankin Ikorodu a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Wasu miyagu sun buɗe wuta a kusa da gidan Ministan Tinubu, sahihan bayanai sun fito

Benjamin Hundeyin.
An kama wani ango da ya kashe amaryarsa a jihar Legas Hoto: Benjamin Hundeyin
Asali: Twitter

Kamar yadda Punch ta ruwaito, angon ya tafka wannan aika-aika ne ranar Juma'a sakamakon wata zazzafar sa-in-sa da ta shiga tsakanin ma'auratan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ango ya kashe amarya a Legas

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar

Ya bayyana cewa Motunrayo ya caccaka wa amaryar ƴar shekaru 25 wuka sau da dama a lokacin da suke faɗan, ya kulle ta a ɗaki sannan ya banka wuta.

Hundeyin ya kara da cewa wanda ake zargin ya raunata kansa domin nuna kamar ba shi da laifi bayan ya aikata kashe matar, Guardian ta ruwaito.

Ƴan sanda sun kama wanda ake zargin

"Ƴan sanda sun samu rahoto ranar 4 ga watan Oktoba a caji ofis na Ikorodu cewa faɗa ya kaure tsakanin wasu sababbin ma'aurata, Motunrayo Olaniyi da matarsa Olajumoke a gidansu."

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun kutsa daji sun sheke babban ɗan bindiga, sun ceto wani Sarki

"Ana cikin haka ne mijin ya cakawa matar wuka har lahira, sannan ya kulle ta a daki, ya kona ɗakin.
"Nan take ƴan sanda suka kai ɗauki wurin, suka kashe wutar kuma suka ɗauko gawar matar da raunuka a jikinta."

- Benjamin Hundeyin.

Kakakin ƴan sandan ya ce an kwantar da angon a asibitin har ya samu lafiya, sannan aka kama shi.

Gobara ta yi ɓarna a Legas

A wani rahoton kuma mutane da dama sun tafka asara bayan gobara ta tashi a kasuwar katako ta Itamaga a Ikorodu da ke jihar Lagos.

Daraktan hukumar ba da agajin gaggawa, Nosa Okunbor ya ce gobarar ta jawo mummunan asara na miliyoyi a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262