"Ban Son Gulma a Fada": Sabon Sarki Ya Gargadi Fadawansa, Ya Fadi Tsarin Mulkinsa

"Ban Son Gulma a Fada": Sabon Sarki Ya Gargadi Fadawansa, Ya Fadi Tsarin Mulkinsa

  • Sabon basarake a jihar Delta, Obi Epiphany Azinge ya gargadi al'umma game da kawo masa gulma musamman a cikin fadarsa
  • Sabon sarkin da aka naɗa bayan mutuwar tsohon basaraken ya bayyana yadda zai gudanar da mulkinsa a masarautar
  • Wannan na zuwa ne bayan nada shi da aka yi inda ya karbi sandar sarauta a yau Asabar 5 ga watan Oktoban 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Delta - Sabon basarake da aka naɗa a jihar Delta ya yi gargadi kan kawo gulma fadarsa.

Asagba na Asaba, Obi Epiphany Azinge ya ce ba zai taba lamuntar masu kawo gulma musamman fadawa ba.

Basarake ya ja kunnen fadawa game da gulma a fada
Sabon sarkin Asaba, Obi Epiphany Azinge ya gargadi fadawa kan kawo gulma fadarsa. Hoto: Obi Epiphany Azinge.
Asali: Facebook

Basarake ya ja kunnen fadawa kan gulma

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Rundunar tsaro ta yi wa Sanata martani kan neman agajin sojojin haya

Azinge ya fadi haka ne jim kaɗan bayan karbar sandar sarauta a yau Asabar 5 ga watan Oktoban 2024, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Basaraken ya sha alwashin daukar mummunan mataki kan wadanda ke kawo gulma inda ya ce ba zai taba lamuntar haka ba.

Ya yabawa tsohon Sarkin wanda ake kira Asagba na Asaba wanda ya rasu kan irin jagorancinsa a birnin.

"Ina godewa Asgaba na 13 wanda ya rasu da sauran wadanda suka riga mu gidan gaskiya."
"Tabbas muradunsa masu kyau ne wanda shi ya ba mu wasiyya mu cigaba daga inda ya tsaya."
"Zan ba da kofa saboda jin ra'ayin mutane amma ba zan taba lamuntar gulma a fada ba, sannan ina bukatar suka wacce za ta zama mai amfani."

- Obi Epiphany Azinge

Basarake ya nemi hadin kan al'ummarsa

Basaraken ya sha alwashin kawo sauyi kan masarautar da samar da ababan more rayuwa.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun mutu bayan yan bindiga sun cilla musu bam, an dauki mataki mai tsauri

Ya shawarci wadanda suka nemi sarautar tare da su ba shi hadin kai domin ciyar da jihar gaba.

An saka ranar hukunci na karar Aminu Ado

Kun ji cewa Babbar kotun Kano ta zabi ranar 10 ga watan Oktoba, 2024 domin yanke hukunci a ƙarar da aka nemi dakatar da gyara fadar Nassarawa.

Gwamnatin Kano ta buƙaci kotun ta hana Sarki na 15, Aminu Ado Bayero aiwatar da shirinsa na gyaran fadar da yake ciki yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.