'Ba ni da Kudin Sadaki a Yanzu', Gwamna Ya Yi Martani kan Rade Radin Karin Aure

'Ba ni da Kudin Sadaki a Yanzu', Gwamna Ya Yi Martani kan Rade Radin Karin Aure

  • Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya musanta labarin cewa yana shirin kara aure bayan mutuwar matarsa
  • Gwamna Eno ya ce kwata-kwata bai shirya kara aure ba a yanzu saboda ko kudin sadaki ba shi da shi
  • Wannan na zuwa ne bayan mutuwar matarsa, Mrs Patience Eno da ta rasu a ranar 26 ga watan Satumbar 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Akwa Ibom - Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya yi magana kan karin aure da ake ta yaɗawa.

Gwamna Eno ya musanta rade-radin da ake yaɗawa cewa yana shirin kara aure bayan mutuwar matarsa.

Gwamna ya ƙaryata labarin da ake yaɗawa cewa zai kara aure
Gwamna Umo Eno ya ƙaryata labarin kara aurensa da ake yadawa. Hoto: Umo Eno.
Asali: Facebook

Gwamna ya ƙaryata labarin zai kara aure

Kara karanta wannan

Kwamacala: Gwamna ya nada 'yarsa domin maye gurbin matarsa a ofishin 'First Lady'

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya karbi bakwancin Sanata Godswill Akpabio a jihar, kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Eno ya ce a yanzu bai shirya kara aure ba bayan mutuwar matarsa, Mrs Patience Eno da ya rasu, kamar yadda Tribune ta ba da rahoto.

Daga bisani, gwamnan ya ce a yanzu ba shi da kudin sake biyan sadaki domin kara aure a rayuwarsa.

Har ila yau, Gwamna Eno ya bayyana yadda zai cigaba da kewar matarsa har zuwa karshen rayuwarsa.

Gwamna ya shiga jimamin mutuwar matarsa

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki tara da mutuwar matarsa a wani asibiti da ke birnin Uyo a jihar Akwa Ibom.

Gwamnan ya shiga jimami inda ya shafe fiye da mako bai ce komai ba saboda kunci da ya shiga na rashin masoyiyarsa inda ya ce zai yi kewarta har karshen rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 9 da mutuwar matarsa, Gwamna ya bude bakinsa, ya fadi halayen marigayiya

Gwamna ya nada 'yarsa 'First Lady'

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Umo Eno ya nada 'yarsa a matsayin 'First Lady' bayan mutuwar matarsa mai suna Patience Eno.

Gwamnan ya nada 'yar tasa na wucin gadi inda ya ce yana da tabbacin za ta cigaban da gudanar da ayyukan ofishin domin kawo sauyi a jihar.

Wanann na zuwa ne bayan mutuwar matar gwamnan mai suna Fasto Mrs Patience Eno wacce ya rasu a ranar 26 ga watan Satumbar 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.