Jami'an Tsaro Sun Kutsa Daji Sun Sheke Babban Ɗan Bindiga, Sun Ceto Wani Sarki
- Ƴan sanda tare da haɗin guiwar wasu hukumomin tsaro sun kai farmaki sansanin ƴan ta'addan IPOB a jihar Imo
- Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, Henry Okoye ya ce sun ceto wani basarake da wasu mutane da aka yi garkuwa da su
- Kakakin ƴan sanda ya ce dakaru sun kashe wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane wanda ya addabi jama'a a baya-bayan nan a Imo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Imo - Dakarun sashin yaƙi da garkuwa da mutane na rundunar ƴan sanda reshen jihar Imo sun kai samame sansanin mayaƙan kungiyar ƴan aware IPOB/MSN.
Ƴan sandan tare da haɗin guiwar jami'an wasu hukumomin tsaro sun farmaki fitaccen sansanin ƴan ta'addan da ke jejin Ezioha a ƙaramar hukumar Mbaitoli a Imo.
Yan sanda sun ceto wani basarake a Imo
Channels tv ta ce yayin wannan samame, jami'an tsaron sun samu nasarar ceto mutanen da dama da aka yi garkuwa da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin waɗanda dakarun suka kuɓutar har da basaraken kauyen Umuorji Mgbidi da ke yankin ƙaramar hukumar Oru, ɗan kimanin shekara 69.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Imo, Henry Okoye ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Dakaru sun kashe babban ɗan bindiga
Ya ce dakarun tsaron sun yi nasarar kashe ƙasurgumin mai garkuwa da mutane wanda kungiyarsa ta addabi al'ummar jihar Imo a kwanakin baya.
Okoye ya ce jami'an tsaro na isa sansanin ƴan ta'addan, suka buɗe masu wuta, aka yi kazamin artabu wanda garin haka ne aka kashe jagoran ƴan bindigar.
A cewarsa, sauran kuma suka arce domin tsira da rayuwarsu amma jami'an tsaro sun jikkata su.
Kakakin ƴan sandan ya ƙara da cewa an ceto wasu ma'aurata da mutanen da aka yi garkuwa da su a dajin.
"Kayayyakin da aka kwato sun hada da motoci, bindiga guda daya, harsasai 10, bama-bamai guda hudu, tutar Biafra daya da dai sauransu," in ji Okoye.
Yan bindiga sun kashe ɗan sanda a Imo
A wani labarin kuma ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hare-hare a jihar Imo da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.
Miyagun ƴan bindigan a yayin harin da suka kai a ƙaramar hukumar Obowo ta jihar sun hallaka wani jami'in ɗan sanda.
Asali: Legit.ng