Matawalle: Kungiya Ta Fito Ta Nemi Afuwar Ministan Tinubu
- Ƙungiyar APC Akida Forum ta nesanta kanta da zanga-zangar da aka yi a ofishin EFCC domin neman a bincike Bello Matawalle
- Shugaban ƙungiyar a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa tuni suka kori mambobin da suka jagoranci zanga-zangar zuwa ofishin EFCC
- Ya bayyana cewa mambobin ƙungiyar da suka yi zanga-zangar kuɗi aka ba su domin su gudanar da aikin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Ƙungiyar APC Akida Forum ta nemi afuwar ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle.
Ƙungiyar ta nemi afuwar ne kan zanga-zangar da suka yi a baya da kuma neman hukumar EFCC ta yi bincike kan lokacin da ya ke gwamnan jihar Zamfara.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar, Alhaji Farouq Adamu, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar APC ta ba Matawalle haƙuri
Ƙungiyar ta kuma ce ta kori mambobin da suka jagoranci zanga-zangar adawa da ministan zuwa ofishin EFCC, ciki har da wani Mahmud Mohammed, rahoton jaridar Tribune.
Alhaji Farouq Adamu ya ce an kafa wani kwamitin gaggawa da zai binciki zanga-zangar kuma an gano cewa kuɗin da aka ba su ya sanya suka yi zanga-zangar.
A cewarsa, musamman Mahmud Mohammed ya ƙi biyan mutanen da ya ɗauko hayarsu zuwa ofishin na EFCC domin gudanar da zanga-zangar bayan da ya karɓi kudaden da suka kai Naira miliyan 50 domin gudanar da aikin.
"Ƙungiyar APC Akida Forum na son bayar da haƙuri ga ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, dangane da zanga-zangar da muka yi a baya da kiran a gudanar da bincike a kan wa'adinsa a matsayin gwamnan Zamfara."
"Mun nesanta kanmu daga zanga-zangar kuma tuni muka kori mambobin da suka jagoranci zuwa ofishin EFCC, ciki har da Mahmud Mohammed."
- Alhaji Farouq Adamu
EFCC ta magantu kan binciken Matawalle
A wani labarin kuma, kun ji cewa Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta yi magana kan zargin karkatar da kuɗaɗen Zamfara da ake yiwa Bello Matawalle.
Hukumar EFCC ta ba da tabbacin cewa za ta gudanar da bincike kan tsohon gwamnan na jihar Zamfara, kan zargin almubazzaranci da kuɗaɗe a lokacin da yake kan mulki.
Asali: Legit.ng