Bam Ya Fashe a Sakatariyar Jam'iyyar APC, An Samu Bayanai
- Wasu da ake zargin ƴan daba ne sun tayar da ababen fashewa a sakatariyar jam'iyyar APC da ke birnin Port-Harcourt na jihar Rivers
- Lamarin ya auku ne da sanyin safiyar ranar Asabar, 5 ga watan Oktoban 2024 yayin da ake shirin zaɓen ƙananan hukumomin jihar
- Shugaban jam'iyyar APC na jihars ya yi zargin cewa waɗanda suka kai harin yaran Gwamna Siminalayi Fubara na jihar ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Wasu da ake zargin ƴan daba ne, sun tayar da bama-bamai a sakatariyar jam'iyyar APC ta jihar Rivers.
Waɗanda ake zargin dai sun tayar da ababen fashewar ne da sanyin safiyar ranar Asabar a sakatariyar da ke birnin Port-Harcourt, babban birnin jihar.
Wasu faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda harin ya lalata babbar kofar shiga da ɗakin masu tsaro na sakatariyar APC da kuma sassan wani gini da ke kusa da ita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin dai na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar a ranar Asabar, 5 ga watan Oktoban 2024.
APC ta yi magana kan lamarin
Jaridar Leadership ta ce a cikin wani gajeran saƙon SMS da ya aika ga ƴan jarida a jihar, shugaban kwamitin riƙo na jam’iyyar APC, Cif Tony Okocha, ya zargi magoya bayan Gwamna Siminalayi Fubara da kai hari kan sakatariyar.
"Da sanyin safiyar Asabar, sojojin farar hula masu goyon bayan Fubara sun tayar da ababen fashewa a ofishinmu."
"Yunƙuri na biyu na ƙona sakatariyar bai yi nasara ba yayin da jami’an tsaron da ke bakin ƙofar shiga suka yi gaggawar kashe wutar."
- Cif Tony Okocha
Idan dai ba a manta ba jam’iyyar APC ta bayyana cewa ba za ta shiga zaɓen kananan hukumomin da za a gudanar a ranar Asabar ɗin nan ba a faɗin jihar.
Zanga-zanga ta ɓarke a Rivers
A wani labarin kuma, kun ji cewa zanga-zanga ta ɓarke a sakatariyar jam’iyyar PDP da ke birnin Port-Harcourt babban birnin jihar Rivers.
Zanga-zangar da ta ɓarke a ranar Alhamis, 3 ga watan Oktoban 2024 an gudanar da ita ne kan zaɓen ƙananan hukumomin jihar.
Asali: Legit.ng