Garambawul: Malami Ya Shawarci Tinubu kan Ministan da Za a Gaggauta Kora

Garambawul: Malami Ya Shawarci Tinubu kan Ministan da Za a Gaggauta Kora

  • Primate Elijah Babatunde Ayodele ya yi kira da a gaggauta korar ƙaramin ministan man fetur, Heineken Lokpobiri
  • Wannan kiran na Ayodele na zuwa ne a daidai lokacin da farashin man fetur ya tashi a Najeriya, wanda malamin ya yi hasashen cewa zai ƙara tashi
  • Malamin ya bayyana cewa rashin iya aikin Heineken Lokpobiri ya kawo wahalhalu da suka haɗa da tsadar man fetur da ƙarancin man fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta korar ƙaramin ministan man fetur, Heineken Lokpobiri.

Fasto Ayodele ya yi wannan kiran ga Shugaba Tinubu a ranar Juma'a, 4 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan

Daukar nauyin 'yan bindiga: Sanata ya yiwa Gwamnan PDP martani mai zafi

Ayodele ya shawarci Tinubu
Fasto Ayodele ya bukaci Tinubu ya kori Heineken Lokpobiri Hoto: @primate_ayodele, @DOlusegun
Asali: Facebook

Legit.ng ta ce wannan kiran na Fasto Ayodele ya zo ne a dai dai lokacin da ake jiran garambawul ɗin da Tinubu zai yiwa majalisar ministocinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fasto Ayodele ya nemi Tinubu ya kori Lokpobiri

Shugaba Tinubu, wanda ya sha alwashin korar ministocin da ba su taɓuka komai ba, ya ƙi fitowa ya yi magana kan yin garambawul a gwamnatinsa.

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Oluwatosin Osho ya fitar, Faston ya bayyana cewa Lokpobiri ya gaza wajen gudanar da ayyukansa a ɓangaren mai.

Ya bayyana cewa yana ɗaya daga cikin jami’an gwamnati da ke haddasa wahalhalun da ke faruwa a Najeriya.

Malamin ya fito fili ya ce ci gaba da zaman da ministan ke yi a kan kujerarsa illa ce ga al’umma.

"Dole ne gwamnati ta yi abin da ya dace ta hanyar duba ayyukan NNPCL da kuma minista Heineken Lokpobiri, wanda bai san komai ba."

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya caccaki Tinubu kan tafiya hutu kasar waje

"Yana ɗaya daga cikin ministocin da ya kamata a tsige ko sauya su daga ɓangaren nan take. Idan ba haka ba, Najeriya za ta sayi man fetur a kan Naira 1,500 kuma za su shigo da gurɓataccen man fetur saboda sakacin ministan da kuma NNPCL."

- Primate Elijah Ayodele

An shawarci Tinubu kan El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar Mandate Protection Vanguard (MPV) ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin muƙamin minista.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci Tinubu da ya naɗa wasu gogaggun mutane a matsayin ministoci a shirin da yake yi na yiwa majalisar ministocinsa garambawul.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng