Gwamna Ya Roƙi Tinubu Ya Kawo Masa Agaji, Ambaliya Ta Ci Garuruwan Arewa 70

Gwamna Ya Roƙi Tinubu Ya Kawo Masa Agaji, Ambaliya Ta Ci Garuruwan Arewa 70

  • Gwamnatin jihar Kogi ta bukaci gwamnatin tarayya ta kawo mata ɗauki yayin da ambaliyar ruwa ta mamaye garuruwa 70 a jihar
  • Mataimakin gwamnan Kogi, Salifu Oyibo ya ce ɓarnar da ruwan ya yiwa al'umma tana da yawa, ya kamata gwamnatin tarayya ta kawo agaji
  • Salifu Oyibo ya ce ba a rasa rai ko ɗaya sakamakon wannan ibtila'i ba saboda mutane sun bar wuraren tun da wuri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kogi - Gwamnatin jihar Kogi ta roƙi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gaggauta kawo mata ɗauki yayin da ambaliyar ruwa ta tarwatsa garuruwa 70 a jihar.

Mataimakin gwamnan jihar, Salifu Oyibo, ne ya yi wannan roƙo a lokacin da ya kai ziyarar duba ɓarnar da ruwan ya yi a kauyen Edeha.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Uba Sani ta ciyo bashin N36bn a Kaduna? An gano gaskiya

Taswirar jihar Kogi.
Gwamnatin Kogi ta bukaci a kawo ɗauki yayin da ambaliya ta mamaye garuruwa 70 a jihar Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Channels tv ta ruwaito cewa Gwamna Ahmed Usman Ododo ya kafa kwamiti karkashin jagorancin Salifu Oyibo domin kai ɗauki ga waɗanda ambaliyar ta shafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwammatin Kogi ta ce abin ya fi ƙarfinta

Da yake jawabi yayin ziyarar, mataimakin gwamnan ya ce halin da ake ciki a kauyen Edeha da wasu garuruwa da ya biyo ta cikinsu ya fi ƙarfin jihar ita kaɗai.

"A bayyane yake cewa halin da ake ciki yanzu ya fi ƙarfin gwamnatin Kogi, ba za mu iya ɗaukar ɗawainiyar mu kaɗai ba, ambaliyar ta shafi garuruwa sama da 70, gidaje sun nutse a ruwa.
“Har yanzu ba a tantance adadin kadarorin da mutane suka yi asara ba ciki har da gonaki. Saboda haka muna bukatar gwamnatin tarayya ta kawo mana ɗaukin gaggawa a yankunan da lamarin ya shafa."

- In ji mataimakin gwamnan Kogi, Salifu Oyibo.

Kara karanta wannan

Cuta ta ɓarke a jihar Borno bayan ambaliyar ruwan da ta afku, bayanai sun fito

Shin an rasa rayuka a ambaliyar?

Oyibo ya nuna farin cikinsa sakamakon babu wanda ruwan ya ci, yana mai cewa galibin mutanen da abin ya shafa sun koma sansanonin ‘yan gudun hijira da jihar ta kafa.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Ododo za ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin ra ragewa waɗanda ambaliyar ta shafa radadin halin da suka tsinci kansu.

Ya tabbatar da cewa an ɗauki matakan da suka dace a sansanonin ‘yan gudun hijira 48 da aka kafa a fadin jihar, rahoton Tribune.

Ambaliya: Kwalara ta ɓulla a Borno

A wani rahoton kuma gwamnatin Borno ta bayyana cewa an samu ɓullar cutar kwalara a wasu ƙananan hukumomi sakamakon ambaliyar ruwa

Kwamishinan lafiya, Farfesa Baba Gana ya ce gwamnati ta fara kokarin yaƙar cutar tun da wuri domin daƙile yaɗuwarta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel